| Hausa
TURKIYYA
4 minti karatu
Turkiyya ba za ta bari a toshe hanyar ci-gabanta ba: Erdogan
Shugaban Turkiyya ya ce Ankara ba za ta tsaya ta zuba ido tana kallon ƙoƙarin yi wa ƙasar ƙawanya ba, a lokacin da ya yi alƙawarin bin hanyar salama da cim ma zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki.
Turkiyya ba za ta bari a toshe hanyar ci-gabanta ba: Erdogan
Shugaba Erdogan yana jawabi bayan taron majalisar ministoci a Ankara, Turkiyya, a ranar 7 ga Satumba, 2026.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi gargaɗi game da matakan ƙiyayya da nufin yi wa Turkiyya ƙawanya, inda ya ce ƙasar ba za ta bari a toshe hanyarta a matsayin ƙasa mai 'yanci da bunƙasa ba.

“Kada kawaicinmu da kwanciyar hankalinmu su sa wani ya yi tunani yin rawar kai a wani wuri. A waɗannan ƙasashe da muka mayar da su gida ta hanyar bayar da rai da ɗaukan rai, ba za mu yarda wani ya gudanar da wani abu ba,” Erdogan ya faɗa a ranar Litinin bayan taron Majalisar Zartarwa a Fadar Shugaban Kasa a Ankara.

“Ba za mu zauna muna kallo daga gefe ga matakan ƙiyayya da nufin yi wa ƙasarmu ƙawanya a yankinmu ba. Turkiyya ba ta adawa da kowace ƙasa, al'umma, addini, ko al'ada,” in ji shi.

“Muna son ci gaba da tafiyarmu a matsayin ƙasa mai 'yanci da wadata a cikin wannan yanki mai wahala. Ba za mu taɓa yarda a toshe wannan hanya ba,” kamar yadda ya ƙara da bayyanawa.

“Waɗanda suka damu da yadda ƙasarmu take ƙara ƙarfi da kuma ƙoƙarinmu na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinmu ba za su iya juyar da mu daga inda muka dosa ba.”

Haɗin kai da zumunci

“Mun dage wajen yin aiki domin tabbatar da cewa haɗin kai da ƙulla zumunci sun samu gindin zama a faɗin yankinmu mai girma, bisa ga manufarmu ta ƙawance da haɗin kai,” in ji Erdogan.

Dangane da kifewar jirgi a makon da ya gabata a gaɓar tekun garin Girne a Jamhuriyar Cyprus ta Arewa (TRNC), Erdogan ya ce: “Da haɗin gwiwa da TRNC, a halin yanzu muna tallafa wa bincike da jiragen ruwa guda tara da jiragen sama 11.”

“Za mu ci gaba da bunƙasa dangantakarmu da Kungiyar Haɗin Gwiwar Shanghai, wacce muke ganin tana tallafa wa ayyukan Majalisar Dinkin Duniya,” in ji Erdogan, yana magana bayan babban taron ƙungiyar a makon da ya gabata a Kyrgyzstan, inda ya halarta a matsayin baƙon ban-girma.

‘Ƙarya da tuggun' Isra'ila sun tarwatsa ƙoƙarin zaman lafiya”

Ta fuskar rikice-rikice a yankin, Erdogan ya zargi Isra'ila da haddasa yaƙi a Gabas ta Tsakiya da kuma mummunan tasirin da hakan ke da shi.

“Asarar da wannan yaƙi ya haifar da ya faro sakamakon ƙulle-ƙulle da tayar da zaune tsaye na Isra'ila ba su tsaya a kan 'yan Iran kaɗai ba, ba su tsaya a kan ƙasashen Gabas ta Tsakiya da muke da alaƙa da su kaɗai ba, har ma kowa, ko da yana da hannu ko ba shi da hannu,” in ji shi.

Ya kuma zargi Isra'ila da kawo cikas ga yarjejeniyar watan Yuni da nufin kawo ƙarshen yaƙin.

“Ƙarya da tuggun Isra'ila ne suka sa yarjejeniyar Islamabad, wacce ta kawo sauƙi ga dukan yankinmu, ta zama ba ta aiki,” in ji Erdogan.

Ci gaba da tafiyar tattalin arzikin Turkiyya

“Guguwar rikice-rikice a yankinmu ba za ta lafa ba har sai wannan ra'ayin mai tsanani, wanda ke kallon kowane ƙaramin yiwuwar zaman lafiya a matsayin barazana, ya canza,” in ji shugaban.

Duk da hayaniya da tashin hankali a yankin, Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da tafiyar da tattalin arzikinta a hanyar bunƙasa da haɓaka.

“Ko da yake muna yin wasu gyare-gyare ga burukanmu, muna ci gaba da wanzar da tattalin arzikin Turkiyya a kan hanyar ci gaba da bunƙasa,” in ji shi.

“Za mu ci gaba da ɗaukar matakai da za su ƙara wadata ga al'ummarmu kuma su samar da mafita ta din-din-din ga matsalolin tsarin tattalin arzikinmu,” a cewar Erdogan.

“Za mu yi duk abin da ya zama dole don sa tattalin arzikin Turkiyya ya zama ƙarfi, mai goyayya, kuma mai juriya a kowane fanni,” in ji shi.

.

Rumbun Labarai
Turkiyya ta yi wa Nijeriya ta’aziyya kan hatsarin jirgin soji
Shelar Antalya da Turkiyya ke jagoranta ta haɗa ƙasashe 21 a haɗin kan lumana kan sararin samaniya
Emine Erdoğan ta jagoranci kiran matan shugabannin duniya na son MDD tai tsarin kare yara a intanet
Turkiyya za ta ci gaba da magana kan Falasɗinawa: Erdogan
Zauren kotu ya dace da masu aikata laifukan yaƙi ba zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba: Erdogan
Jami’an Sojin Ruwa 30 na Saudiyya sun kammala karɓar horo a kamfanin tsaron Turkiyya, Baykar
Yadda Turkiyya ke taimaka wa Iraƙi wajen isar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa
An wallafa jawabin Shugaba Erdogan na UNGA-81 a matsayin littafi cikin harsuna uku
Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya
Emine Erdogan ta buƙaci a rabu da ‘al’adar jefar da kaya' a koma ga tsarin sabuntawa
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Abincin Afirka daga Turkiyya
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya
'Turkiyya za ta duba buƙatun Saudiyya ƙarƙashin yarjejeniyar Makkah yayin da Houthi ke kai hari'
An gano kwanson wani dodon koɗi mai shekara 66,000 a Ankara babban birnin Turkiyya
Turkiyya ta yi zarra a Shirin Ƙimar Dalibai na Duniya (PISA) 2025 a tsakanin ƙasashen OECD
Turkiyya ta yi Allah wadai kan girmama Ratko Mladic da aka yanke wa hukuncin laifin yaƙi
Jiragen ruwa biyu na kasuwanci sun yi karo a gabar Tekun Silivri a Istanbul, mutum 10 sun ɓata
30 ga Agusta: Nasarar da ta buɗe hanyar tasowar Turkiyya ta zamani
An haƙo wani sassaƙen ɗan'adam zaune a kan damisa mai shekaru 11,000 a Turkiyya