Kotun Ƙolin Nijeriya ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda ta tabbatar da hukuncin kisa

A watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya yi wa Maryam afuwa ta hanyar sassauta mata hukuncin daga na kisa zuwa na zaman gida yari na shekaru 12 a bisa dalilai na tausayawa.

By
Maryam Sanda / Others

Kotun Ƙolin Nijeriya ta soke afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, wacce aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya a shekarar 2020 saboda kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

A hukuncin da ta yanke a ranar Jumma’a a babban birnin ƙasar Abuja, Kotun Kolin ta sake tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Maryam Sanda.

A watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya yi wa Maryam afuwa ta hanyar sassauta mata hukuncin daga na kisa zuwa na zaman gida yari na shekaru 12 a bisa dalilai na tausayawa.

Kotun Koli ta warware dukkan batutuwan da aka gabatar a cikin ɗaukaka ƙarar da ta shigar a kanta kuma ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta.

Alkali Moore Adumein wanda ya jagoranci yanke hukuncin ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da shari'ar ba tare da wata shakka ba kamar yadda ake bukata, inda ya ƙara da cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi daidai da ta tabbatar da hukuncin da kotun farko ta yanke.

Mai Shari'a Adumein ya yanke hukuncin cewa ba daidai ba ne Shugaban Kasa ya nemi yin amfani da ikon yin afuwa kan wata shari'ar kisan kai da aka aikata, wadda ake jiran hukuncin ƙarar da aka ɗaukaka a kanta.