| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Wane kasashe biyu ne za su so faduwa wasansu na karshe a rukunin gasar Kofin Duniya?
Ga Algeria, yin nasara a wasan zai ba su matsayi na biyu a Rukunin tare da yiwuwar karawa da Sifaniya; yayin da canjaras ko rashin nasara zai ba su garantin matsayi na uku a Rukunin.
Wane kasashe biyu ne za su so faduwa wasansu na karshe a rukunin gasar Kofin Duniya?
Ranar 28 ga Yuni za a fara zagayen 'yan 32 na siri-ɗaya-ƙwale a gasar ta FIFA 2026. / AP

Yayin da ake kammala zagayen ƙarshe na wasannin rukuni a gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 da ke guda a Amurka, Canada, da Mexico, tuni wasu ƙasashe suka wuce mataki na gaba, amma wasu na ƙoƙarin neman cancanta har yanzu.

A wasa na uku na Rukunoni, akwai ƙasashen da ke neman zuwa na biyu a teburi, yayin da masu neman samun na uku suke fatan samun ƙwaƙƙwaran matsayin da zai ba su damar shiga sahun ƙasashe takwas da suka fi nuna bajinta cikin waɗanda suka zo na uku.

A Rukunin J, ƙasar Argentina tana da maki shida da ya kai ta matakin gaba, a zahiri ƙasashen Algeria da Austria suna fafutukar neman matsayi na biyu don samun gurbi a matakin na gaba.

Tuni dai ƙasa ta huɗu a rukunin, wato Jordan wadda ba ta da maki ko guda bayan wasanni biyu, ta rasa damar kai wa matakin gaba. Kenan fafutuka ta rage tsakanin Algeria da Austria waɗanda ke da maki uku kowannensu.

Sai dai masu sharhi na cewa ƙasashen na Algeria da Austria, za su fi son su raba maki tsakaninsu a wasan da za su buga ranar Lahadi mai zuwa. Wato dai babu mai son yin nasara a wasan da ya kamata ya fayyace waye na biyu kuma waye na uku.

Hasali ma, ga Austria, faɗuwa za ta fi mata amfani sama da canjaras ko yin nasara a wasan da za a yi a birnin Kansas City.

Kasancewar kowannensu ya doke Jordan, ko da sun ƙare da maki ɗai-ɗai, to za su kasance a saman Jordan ɗin.

Wannan ne ya sa ƙasar da ta zo ta biyu a Rukunin na J ta yiwu ta kara da Sifaniya a wasan matakin gaba, yayin da ƙasa ta uku a Rukunin, za ta haɗu da wata ƙasar da ba za ta kai Sifaniya haɗari ba.

Ga Algeria, yin nasara a wasan zai ba su matsayi na biyu a Rukunin da yiwuwar karawa da Sifaniya; yayin da canjaras ko rashin nasara zai ba su garantin matsayi na uku a Rukunin.

Sai dai ga Austria, wadda a yanzu take matsayi na biyu akasancewar tana da fifikon yawan ƙwallo, dole sai sun faɗo ƙasan Algeria don zamowa na uku a Rukunin.

Wato dai waɗannan dalilai ne za su iya sa duka ƙasashen biyu su nemi ƙarewa a mataki na uku, maimakon na biyu a Rukuni.

Sai dai kasancewa za a yi wasan na ƙarshe a Rukunin na J bayan kowane guruf na gasar ya kammala wasansa, Austria da Algeria za su san matsayarsu kafin wasan nasu.

A tarihi an taɓa ganin irin wannan yanayi a gasar Kofin Duniya na 1982, lokacin da West Germany da Austria suka gane cewa ƙaramar nasara ga West German zai kai duka ƙasashen mataki na gaba.

A wasan nasu, West Germany ta ci ƙwallo ɗaya da wuri, sannan daga nan sai ‘yanwasan ƙasashen biyu suka fara fasin-fasin a tsakiyar fili, har aka gane a fili ba wanda matsawa don ƙoƙarin cin ƙwallo.

A ƙarshe Algeria ta shigar da ƙorafi gaban FIFA, kuma hakan ya sa hukumar ta yanke cewa dole a buga wasanni ƙarshe na rukuni a tare a duka gasanni tun daga shekarar ta 1982.