| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
EFCC ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin wani taro da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yanjarida.
EFCC ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya
EFCC

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Masu Laifin Tattalin Arziki ta Nijeriya, EFCC ta ce ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa da kuma almundahana cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin wani taro da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yanjarida.

Ya ce fiye da biyar daga cikin ma’aikatan da aka kora a halin yanzu suna fuskantar shari’a, yayin da ake shirya takardun shari’ar wasu da ake zargi da aikata laifuka.

Olukoyede ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa ma’aikatan hukumar suna bin ƙa’idojin gaskiya da riƙon amana.

Hukumar ta kuma ƙaddamar da dokar karɓar kyaututtuka, wadda ke buƙatar ma’aikata su bayyana kadarori da kyaututtukan da suka wuce wani ƙayyadadden ƙima, ciki har da kyaututtukan da suka samu daga ’yan’uwa da ke ƙasashen waje.

Haka kuma, EFCC ta sauya sunan tsohon Sashen Harkokin Cikin Gida zuwa Sashen Da’a da Riƙon Amana, domin ƙarfafa sa ido da ɗa’a a cikin hukumar.

Olukoyede ya kuma bayyana cewa EFCC ta ƙwato kusan naira tiriliyan 1.23 da dala miliyan 684.48 da fam 373,905 da kuma euro miliyan 9.34 tsakanin 1 ga Oktoban 2023 zuwa 30 ga Yuni 2026.

Daga cikin kuɗin naira da aka ƙwato, kusan N397.26 biliyan an kwato su kai tsaye ga gwamnatin tarayya, yayin da N836.34 biliyan aka kwato a madadin ma’aikatun gwamnati, hukumomi, jihohi, kamfanoni, da wasu mutane da waɗanda laifukan suka shafa a ƙasashen waje.

Ya ce fiye da N661 biliyan da dala miliyan 492 daga cikin kuɗin da aka ƙwato an riga an miƙa su ga waɗanda suka cancanci karɓa.

Shugaban EFCC ya jaddada cewa ma’aikatan hukumar ba za su iya yaƙar cin hanci da rashawa yadda ya kamata ba, alhali su kansu suna aikata irin wannan laifi.