| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An saki ragowar ɗaliban St. Mary’s 130 da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja: gwamnatin Nijeriya
Mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara na musamman kan harkokin watsa labarai Bayo Onanuga ya wallafa hotunan ɗaliban a cikin motocin bas biyu a shafinsa na X, inda ya ce ana sa ran za su ƙarasa Minna babban birnin Jihar Neja ranar Litinin.
An saki ragowar ɗaliban St. Mary’s 130 da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja: gwamnatin Nijeriya
A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025, wasu ‘yanbindiga a kan babura suka kai hari a St. Mary’s Catholic School inda suka sace mutum 315 / AP
22 Disamba 2025

Gwamnatin Nijeriya ta ce an saki ragowar ɗalibai 130 na makarantar sakandaren St Mary’s da ke Papiri a Jihar Neja, waɗanda ‘yanbindiga suka yi garkuwa da su a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara na musamman kan harkokin watsa labarai Bayo Onanuga ne ya wallafa hotunan ɗaliban a cikin motocin bas biyu ranar Lahadi a shafinsa na X.

Ya ce ana sa ran za su ƙarasa Minna babban birnin Jihar Neja ranar Litinin.

Ya ce dama tuni aka saki 100, abin da ya kai adadin ɗaliban da aka saki zuwa 230.

Onanuga ya ce an saki ɗaliban ne sakamakon aikin ɓangaren tattara bayanan sirri na rundunar sojin Nijeriya.

Masu AlakaGwamnatin Jihar Neja ta karɓi ɗalibai 100 na St. Mary’s Catholic School da aka ceto - TRT Afrika Hausa

Makonni biyu da suka wuce, gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya tarbi ɗalibai 100 na makarantar St. Mary waɗanda ofishin mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan sha’anin tsaro ne ya miƙa masa bayan an kuɓutar da su daga wurin masu garkuwa da mutane.

A jawabinsa ya yi miƙa ɗaliban a wancan lokacin, Wing Commander Abdullahi Dare ya ce ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro tare da haɗin gwiwar dakarun sojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro ne suka kuɓutar da ɗaliban.

A nasa jawabin, Gwamna Bago ya gode wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro da dukkan jami’an tsaron ƙasar da ma masu ruwa da tsaki kan rawar da suka taka wajen kuɓutar da ɗalibai 100.

Tun da farko ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN, ta hannun shugabanta reshen Jihar Neja, Bishop Bulus Yohanna, ta ce ba ta samu bayanai a hukumance ba kan kuɓutar da ɗaliban.

A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025, wasu ‘yanbindiga a kan babura suka kai hari a St. Mary’s Catholic School inda suka sace mutum 315 —ɗalibai 303 da malamai 12.

Jami’an tsaro da mafarauta sun fantsama cikin dajin yankin inda suka yi ta neman mutanen da aka sace.

Daga bisani, hukumomin makarantar sun ce ɗalibai aƙalla 50 sun tsere daga masu garkuwa da mutanen inda suka koma wurin iyayensu.

MAJIYA:AFP