‘Yanwasa shida ‘yan gida-daya da ke buga Gasar Kofin Duniya
Désiré Doué da Guéla Doué sun fuskanci juna yayin da Faransa da Ivory Coast suka fafata a wasan sada zumunta gabanin gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026. / APA News Agency
‘Yanwasa shida ‘yan gida-daya da ke buga Gasar Kofin Duniya
Wasu 'yanwasan 'yan gida-ɗaya sukan bazama neman damarmaki a wajen ƙasar da aka haife su, inda a ƙarshe wani kan shiga tawagar ƙasa daban da ta ɗan-uwansa.

A gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 da ke gudana a Amurka, Canada, da Mexico, akwai ‘yanwasa yan gida-ɗaya da ke buga gasar tare, wasu a tawaga guda, wasu kuma na wakiltar ƙasashe mabambanta. Ga labarin wasu cikin rin waɗannan ‘yanwasa shida.

Iñaki Williams da Nico Williams

Iñaki da Nico Williams sun girma tare a Sifaniya har suka buga wasa a Athletic Club, amma da suka tashi shiga tawagar ƙasa-da-ƙasa, sai suka raba gari.

Nico Williams ya zaɓi Sifaniya, shi kuma Iñaki ya shiga tawagar Ghana, ƙasar da aka haifi iyayensu, Félix Williams da María Arthuer. A yanzu haka, ‘yanwasan biyu suna buga wa ƙasashe biyu gasar Kofin duniya ta FIFA 2026.

Désiré Doué da Guéla Doué

Désiré da Guéla Doué ‘yan gida ɗaya ne da suka girma tare. Iyayensu ‘yan asalin Ivory Coast ne da suka yi hijira zuwa Faransa. Désiré da Guéla sun fara buga ƙwallo a Stade Rennais ta Faransa.

Désiré ya zama tauraro a PSG, sannan ya shiga tawagar Faransa. Shi kuwa Guéla, ya zaɓi buga wa Ivory Coast, kuma su biyun duka a halin yanzu suna buga gasar Kofin Duniya, amma sanye da mabambantan jesi.

 Derrick Luckassen da Brian Brobbey

Mahaifiyar Derrick da Brian Brobbey ta haife su a Netherlands, amma ubansu daban-daban. Sun fara ƙwallo tun suna matasa a Netherlands, amma sai suka zaɓi shiga tawagar ƙasa daban.

Brian Brobbey ya zaɓi buga wa tawagar Netherlands, yayin da Derrick Luckassen yake buga wa ƙasar da suke da tsatso, wato Ghana, kuma a yanzu sun haɗe a gasar Kofin Duniya.

 John Souttar da Harry Souttar

An haifi John da Harry Souttar a Aberdeen, Scotland, kuma dukansu suna buga ƙwallo a matsayin masu tsaron baya.

Sai dai kasancewar suna da tsatson Scotland da Australia, John ya shiga tawagar Scotland, yayin da Harry yake wakiltar Australia, kuma har ya buga musu Kofin Duniya na 2022, kafin su haɗu a kakar bana.

Laros Duarte da Deroy Duarte

Laros da Deroy Duarte sun kwashe lokacinsu na ƙwallo a Netherlands, amma da lokacin shigarsu tawagar ƙasa ya yi, dukkansu sun zaɓi buga wa ƙasarsu ta asali, Cape Verde wasa.

Hasali ma, yawancin ‘yan tawagar ƙasar ta Cape Verde, wadda yanzu ake kira da Cabo Verde, a Netherlands suke taka leda.

Lucas Hernández da Theo Hernández

Lucas da Theo Hernández suna buga wa tawagar Sifaniya a tare, duk da cewa Lucas ne ya fara shiga tawagar, har ma ya ɗaga Kofin Duniya lokacin da Faransa ta lashe kofin a 2018.

A halin yanzu dai ‘yan gida ɗayan za su yi ƙoƙarin haɗa-kai don lashe gasar ta bana.