| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
INEC ta yi ƙarin haske kan cire sunayen wasu ‘yantakarar gwamna a zaɓen 2027
Cire sunayen 'yantakarar ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli da bayyana cewa jam’iyyun da suka gaza cika ƙa'idojin da doka ta tanada ba su da hurumin tsayar da 'yantakara a zaɓen, a cewar Hukumar INEC.
INEC ta yi ƙarin haske kan cire sunayen wasu ‘yantakarar gwamna a zaɓen 2027
Hukumar INEC ta jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya da bin doka da kuma amincin tsarin zabe.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya (INEC) ta yi ƙarin haske game da cire sunayen wasu 'yantakara daga jerin sunayen ƙarshe na zaɓen gwamna na shekarar 2027, tana mai kafa hujja da cewa jam'iyyunsu sun gaza gabatar da rajistar mambobinsu kamar yadda doka ta tanada.

Wannan ƙarin bayani ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ce-ce-ku-ce daga waɗanda abin ya shafa bayan wallafa jerin sunayen ƙarshe, wanda bai haɗa da wasu fitattun ’yantakara ba, ciki har da ’yantakarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihohin Gombe da Ogun, wato Isa Pantami da Ladi Adebutu na PDP a jihar Ogun.

Da kuma Abdussalam Aminu Gwarzo na NDC a jihar Kano

A ƙarshen makon jiya ne dai INEC ta fitar da sunyen ‘yantakarar gwaman inda ta cire sunan Pantami daga cikin jerin sunayen bayan da ya lashe zaɓen fid da gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Gombe, wanda kotu ta bayar da umarnin a yi.

Haka kuma, ba a saka sunan Abdussalam Aminu Gwarzo da Adebutu ba a cikin jerin sunayen ba.

A ƙorafin da ya yi ta hannun lauyoyinsa, Isa Ali Pantami ya bai wa INEC kwanaki biyu da ta saka sunansa a cikin ‘yantakarar gwamna na jihar Gombe.

Kazalika jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar NDC, Yusif Fasaha ya ce matsalar rashin saka sunan Abdussalam Aminu Gwarzo ba daga jam’iyyar ba ce, yana mai cewa NDC ta tuntunɓi INEC kuma hukumar ta shaida mata cewa matsala ce ta na’ura za ta gyara.

Ita kuma jam’iyyar PDP reshen jihar Ogun ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da matsa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) lamba saboda ta hana saka sunan ɗantakararta a cikin jerin sunayen.

Masu AlakaTRT Afrika - Pantami ya bai wa INEC wa’adin kwana biyu ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar gwamnan Gombe

Martanin INEC

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa na INEC kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu a ranar Talata, hukumar ta ce cire sunayen ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026.

Hukuncin, wanda aka yanke a shari’ar INEC da Zenith Labour Party, mai lamba SC/CV/495/2026, ya tabbatar da cewa sashe na 77(5) zuwa (7) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya dace da kundin tsarin mulki.

Waɗannan tanade-tanade sun wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa rajistar mambobinsu ga hukumar cikin wa’adin da aka ƙayyade.

Kotun ta kuma tabbatar da ingancin jadawalin INEC da ya tanadi cewa jam’iyyun su miƙa rajistar mambobinsu tsakanin 21 ga Afrilu zuwa 10 ga Mayu, 2026.

A cewar hukumar, Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa jam’iyyun da suka gaza cika waɗannan ƙa'idoji ba su da hurumin tsayar da 'yantakara a zaɓen.

INEC ta ce ta yi amfani da wannan hukunci wajen kammala fitar da jerin sunayen ’yantakarar gwamna, bisa tanadin sashe na 287(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima.

Kazalika, Hukumar ta bayyana cewa an wallafa jerin sunayen ’yantakarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa na ƙarshe a ranar 12 ga Satumba, 2026, wato kwanaki 13 kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukuncinta.

Sannan ta ƙara da cewa, bisa sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, jam’iyyun siyasa da ke ganin an cire sunayen ’yantakararsu bisa kuskure suna da kwanaki 14 daga ranar wallafa jerin sunayen domin sanar da hukumar.

INEC ta sanya ranar 24 ga Oktoba, 2026, a matsayin wa’adin ƙarshe na miƙa irin waɗannan sanarwa.

Hukumar ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana, bin doka da oda, da kuma sahihancin tsarin zaɓe.