Turkiyya ta yi tir da Israila kan amincewa da Somaliland

Turkiyya ta yi kakkausar suka kan matakin Isra'ila na amince wa da Somaliland a matsayin kasa mai 'yancin kai.

By
Turkish Head of Communications Burhanettin Duran says Israel's recognition of Somaliland is a violation of Somalia's sovereignty. / AA

Turkiyya ta yi kakkausar suka kan matakin Isra'ila na amince wa da Somaliland a matsayin kasa mai 'yancin kai.

A ranar Juma'a, Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta bayyana matakin na Tel Aviv a matsayin "keta doka ta ƙasa da ƙasa ƙarar" da kuma "tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Somaliya."

"Wannan mataki yana nufin kai hari ga 'yancin kai da cikakken ikon ƙasa na Somaliya, kuma zai ara ƙara taɓarɓara yanayin da ke ciki yankin (Kusurwar Afirka) wanda yake da rauni," in ji Burhanettin Duran, Shugaban Sadarwa na Turkiyya.

"Wannan matsayi na daga cikin ayyukan rashin tunani na gwamnatin (Firaministan Isra'ila Benjamin) Netanyahu, wadda ke da baƙin tarihin na kisan aƙre dangi da mamaya, kuma wadda ke daƙile yunuƙrin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin," in ji Duran a cikin wata sanarwar da aka fitar a hukumance.

Allah wadai a matakin duniya

Yayin da yake sake jaddada goyon bayan Turkiyya ga 'yancin Somaliya, Shugaban Sadarwar na Turkiyya ya ce: "Ina ga ya kamata al'ummar duniya ta ɗauki matsaya ɗaya kan irin waɗannan matakai waɗanda za su ƙara dagula al'amura da kuma ƙara dagular matsalar tsaro a Kusurwar Afirka."

A ranar Juma'a, matakin Isra'ila ya jawo suka daga duniya baki daya, ciki har da Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), da Ƙungiyar Haɗin Kan Larabawa, da Hukumar Falasdinu, saboda ta amince da Somaliland, wani yanki a arewacin Somaliya wanda yake cikin iyakokin Jamhuriyar Tarayyar Somaliya.

A nata ɓangaren, Somaliya ta yi tir da wannan mataki na tsokana na Isra'ila, inda ta bayyana matakin Tel Aviv a matsayin keta 'yancinta da cikakken ikon yankinta.