| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Ƙungiyar EU ta sanar da sanya sabbin takunkumai kan cinikayyar zinare a Sudan
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta gabatar da wasu sabbin takunkumai da suka shafi cinikayyar zinare a Sudan da kuma taƙaita damar samun sinadarai da ake amfani da su a haƙar zinare.
Ƙungiyar EU ta sanar da sanya sabbin takunkumai kan cinikayyar zinare a Sudan
"Zinare ya zama babban tushe na samun kuɗin shiga wanda ke ci gaba da rura matsalar tashin hankali a Sudan," a cewar Majalisar Tarayyar Turai,

Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ranar Litinin ta sanya sabbin takunkumai da suka shafi cinikayyar zinare na Sudan da kuma taƙaita damar samun sinadarai da ake amfani da su a haƙar zinare.

Ta ce ta ɗauki matakin ne domin katse kuɗi da ke tallafa wa rikici da tashe-tashen hankula a Sudan da kuma ƙara matsin lamba ga waɗanda ake zargi da rura wutar yaƙin, a cewar wata sanarwa daga Majalisar EU.

A ƙarƙashin matakai dai, ƙungiyar EU ta haramta saye da shigowa da kayayyaki da kuma jigilar zinare daga Sudan, yayin da kuma ta haramta sayarwa, samarwa, canja wuri, da kuma fitar da sinadarin mercury da cyanide a ƙasar.

Kazalika takunkuman sun haɗa da ayyukan da suka shafi samun taimakon fasaha da ayyukan dillalai da tallafin kuɗi da ke da alaƙa da kayayyakin da aka haramta.

Rikicin jinƙai 

"Zinare ya zama babbar hanyar samun kuɗin shiga wanda ke ci gaba da rura matsalar tashin hankali a Sudan," a cewar Majalisar Tarayyar Turai.

Majalisar ta ƙara da cewa, taƙaita kasuwancin zinare a Sudan da kuma samun sinadarai da ake amfani da su wajen haƙar zinare za su rage albarkatun da ke shiga hannun waɗanda ke da alhakin ci gaba da yaƙin da ya dabaibaye Sudan.

Tun a watan Afrilun 2023 ne Sudan ta tsunduma cikin yaƙi, bayan ɓarkewar faɗa a tsakanin sojoji da kuma Rundunar dakarun sa-kai ta (RSF) kan shirin haɗa rundunar cikin sojojin ƙasar.

Yaƙin ya haifar da ɗaya daga cikin rikice-rikicen jinƙai mafiya muni a duniya, inda ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.