| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya dakatar da shirinsa na taimaka wa jiragen ruwa wucewa ta Mashigar Hormuz
Shugaban Amurka ya ce Washington za ta dakatar da ayyukanta na wucin-gadi yayin da take ci gaba da yi wa Iran ƙawanya, yana mai iƙirarin cewa "an samu gagarumin ci-gaba wajen samun cikakkiyar yarjejeniya ta ƙarshe da wakilan Iran."
Trump ya dakatar da shirinsa na taimaka wa jiragen ruwa wucewa ta Mashigar Hormuz
Trump ya yi shelar dakatar da “Aikin 'Yanci” a mashigin ruwan Hormuz, inda yaka nuna an samu “gagarumar ci-gaba ” a yarjejeniyar zaman lafiya da Iran. / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya dakatar da ayyukan sojin Amurka na raka jiragen ruwa ta Mashigar ruwan Hormuz bayan kwana ɗaya kawai, a wani mataki na ƙulla yarjejeniya da Iran domin kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya.

"Za a dakatar da Aikin ‘Yanci (Tafiyar jiragen ruwa ta mashigar ruwan Hormuz) na ƙanƙanen lokaci domin ganin ko za a iya tabbatar da yarjejeniya da kuma rattaba hannu a kanta ko kuma hakan ba zai yiwu ba," kamar yadda Trump ya bayyana a shafin sada zumuntansa na Truth Social.

Yayin da yake ishara ga kiraye-kiraye daga Pakistan da sauran ƙasashe, tare da ci-gaban da aka samu na cim ma yarjejeniya ta ƙarshe da Tehran, Trump ya yi shelar shawara ta baya bayan nan da aka yanke, amma ya haƙiƙance cewa ƙawanya ta sojin ruwa za ta ci gaba da aiki.

Tun da farko dai, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce matakin yaƙi da Amurka ta ƙaddamar kan Iran a watan Fabrairu ya ƙare kuma a yanzu Amurka ta mayar da hankali ne kan wani sabon aiki na raka jiragen ruwa ta mashigar ruwan Hormuz.

Yiwuwar ƙulla yarjejeniya da Iran

A ranar Litinin ne Trump ya yi shelar “Aikin ‘Yanci”, kuma ana tsammanin aikin zai taimaka wa jiragen ruwa daga ƙasashen da ba sa cikin yaƙin da Iran su iya wucewa cikin aminci ta mashigar ruwan Hormuz.

Aikin da hedkwatar sojin Amurka (CENTCOM) ke yi ya ƙunshi na’urori masu lalata makamai masu linzami da jiragen sama fiye da 100, da jirage mara matuƙa da kuma dubban ma’aikata da ke ba da jagoranci da kauce wa nakiya da kuma kasancewa cikin shiri na kare jiragen ruwa na ‘yankasuwa da ba su da cikakkun ‘yan rakiya.

An yi shirin ne domin warware toshe mashigar da Iran ta yi inda ta katse gudanar mai a duniya kuma an bayyana shi a matsayin wani taƙaitaccen mataki na kariya da ya mayar da hankali kan ‘yancin tafiya ta ruwa da kuma kare tafiyar jiragen ruwa da ba su ji ba ba su gani ba.

Aikin dai ya fuskanci tsaiko daga farko inda aka yi musayar wuta, amma yanzu an dakatar da shi domin ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya domin yiwuwar ƙulla yarjejeniya da Iran.