Farashin zinare ya fadi matuka. Ga nahiyar Afirka, wannan babban lamari ne. A ranar 18 ga Nuwamba, farashin zinare ya sauka kasa da dala 3,800 kan kowane oza karon farko cikin shekara guda, inda ya tsaya a dala 3,792.
Ga kasashen da ke hako zinare kamar Ghana, Afirka ta Kudu, Mali, Burkina Faso, Guinea, Tanzania da Sudan, wannan ba kawai wani adadi ne da ake gani a kasuwar hada-hadar zinare ba.
Zinare na da matukar muhimmanci wajen samar musu da kudaden shiga a dalar Amurka, gudanar da kasafin kudinsu da kuma kare darajar kudaden kasashensu.
A Mali da Burkina Faso, zinare ne babbar hanyar samun kudaden shiga daga fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Ita kuwa Ghana, yanzu tana samun karin kudaden shiga daga zinare fiye da koko.
A watan Satumba, Burkina Faso ta kaddamar da matatar zinare domin rage fitar da danyen sa zuwa kasashen waje da kuma kara darajar kayayyakin da take sarrafawa a cikin gida. Bayan wata guda, Guinea ma ta dauki irin wannan matakin. Wannan wani shiri ne na dogon lokaci.
A dunkule, faduwar farashin zinaren da ya haura kashi daya bisa hudu tun daga karshen watan Fabrairu na iya yin illa ga kudaden shigar kasashen da ke hako shi.
Hakan na nufin karancin kudaden shiga daga fitar da zinare, raguwar kudaden harajin hakar ma'adinai da kuma karancin kudaden kasashen waje.
Sai dai wannan faduwar farashi ba tana nufin cewa zinare ya rasa darajarsa ba ne. A farashin dala 3,792 kan kowane oza, har yanzu zinare na kan farashi mai matukar tsada idan aka kwatanta da tarihin farashinsa.
Shekaru uku da suka gabata, farashin zinare na tsakanin dala 1,800 zuwa dala 2,000 kan kowane oza. Yawancin manyan kamfanonin hakar zinariya har yanzu suna iya samun riba.
Abin da ya ɓace shi ne hauhawar farashin da ya kai kololuwa a farkon shekarar 2026, saboda tsananin sha'awar masu zuba jari a fannin zinaren.
A watan Janairu, farashin zinaren ya yi tashin gwauron zabi sakamakon sayen zinaren da manyan bankunan duniya suka yi, fargabar matsalolin tattalin arziki da kuma sassauta manufofin hada-hadar kudi.
Hare-Haren Amurka da Isra’ila
A ranar 29 ga Janairu, farashin zinare ya kai wani sabon matsayi mafi girma a tarihi, inda ya kai kusan dala 5,600 kan kowane oza.
A watan Fabrairu, matsakaicin farashinsa ya kai dala 5,020, wanda shi ne mafi girma da aka taba samu a kowane wata.
Hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran a karshen watan Fabrairu su ma sun sanya farashin zinare cikin tashin gwauron zabi da faduwa.
Da farko, hare-haren sun sa farashin zinare ya tashi, yayin da mutane suka yi tururuwa wajen sayen kadarorin da ake ganin sun fi aminci a lokacin rikici.
Amma daga baya, hare-haren sun haifar da karin tashin farashin man fetur, wanda ya kara tsananta hauhawar farashin kayayyaki tare da sa bankunan tsakiya suka karkata ga tsaurara manufofin kudi maimakon sassauta su.
Irin wannan tsaurara manufofin kudi shi ne babban abin da ke kawo cikas ga karin darajar zinare.
Zinare ba ya samar da ribar ruwa kamar wasu zuba jarin. Idan ribar takardun bashin gwamnatin Amurka ta haura kashi biyar cikin dari, sannan darajar dalar Amurka ta yi tashin gwauron zabi, masu zuba jari kan sayar da zinarensu su koma sayen daloli da takardun bashi.
A wannan makon, Shugaban babban bankin Tarayya na Amurka (Fed) a St. Louis, Alberto Musalem, ya bayyana cewa Amurka za ta bukaci karin wasu matakan daga cikin manufofin tsaurara kudin ruwa kafin bazara, yayin da kasuwannin hada-hadar kudi ke hasashen yiwuwar karin kudin ruwa a watan Disamba.
Darajar dalar Amurka ta yi tashi zuwa mataki mafi girma tun watan Afrilun 2025.
Ga kasashen Afirka masu hako zinare, sakamakon hakan shi ne tsaurara kasafin kudi, raunana darajar kudaden kasashensu, jinkirta ayyukan raya kasa da kuma matsin lamba kan ma'adinan da ke da tsadar hakowa da kuma ayyukan yi.
Idan farashin zinare ya ci gaba da kasancewa a kasa da dala 4,000 kan kowane oza, matsin tattalin arzikin zai kara tsananta.
Sai dai manyan bankunan kasashe na ci gaba da sayen zinare, yayin da bukatar zinare da ake amfani da shi wajen kera kayan ado ke nan daram.
Haka kuma, ana amfani da zinare wajen kera na'urorin lantarki, aikin likitan hakora, magunguna da kuma fasahar sararin samaniya. Wadannan abubuwa na nufin cewa farashin zinare na iya sake farfadowa.
Amma a halin yanzu, zamanin da ake samun farashin zinare na dala 5,000 kan kowane oza ya wuce.
Kasashen da suka fi cin moriyar bunkasar farashinsa kuwa na iya kasancewa cikin wadanda za su fara fuskantar koma bayan da wannan faduwar farashi za ta haifar.






















