| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
CAF ta tabbatar da ranakun buga wasannin kwatafainal na Kofin Zakarun Afrika
Za a buga wasan ƙarshe na Kofin Zakarun Turai na Afirka a watan Mayu don fayyace zakaran kulob ɗin Afirka.
CAF ta tabbatar da ranakun buga wasannin kwatafainal na Kofin Zakarun Afrika
Wasannin za a buga su a zagaye biyu. / Reuters
2 awanni baya

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta tabbatar da ranaku da lokutan fara wasannin kwata-fainal na gasar Zakarun Turai ta CAF ta kakar 2025/26, inda za a buga jerin manyan wasanni a faɗin nahiyar a watan Maris.

Ɗaya daga cikin fitattun wasannin zai haɗa shahararriyar ƙungiyar da ke Masar, Al Ahly, da wata shahararriyar ƙungiyar da ke Tunisia, Espérance Sportive de Tunis. An shirya wasan farko a Tunis ranar 15 ga Maris, sai wasan ramako a Cairo ranar 21 ga Maris.

Kungiyar Afirka ta Kudu, Mamelodi Sundowns, za ta fara kamfen ɗinta na kwata-fainal a gida tare da Stade Malien ta Mali ran 13 ga Maris. Wasa na biyu za a buga shi a Bamako ranar 22 ga Maris.

Pyramids FC ta Masar za ta tunkari AS FAR ta Maroko; inda wasan farko zia gudana a Maroko ranar 13 ga Maris, kafin a dawo da wasan a Masar ranar 21 ga Maris.

Wasu sauran fafatawa su ne: RS Berkane ta Maroko da za ta karɓi baƙuncin ƙungiyar Al Hilal ta Sudan, a wasan farko ranar 14 ga Maris, yayin da wasan ramuwa zai kasance ranar 22 ga Maris.

Sauran wasanni

Za a buga wasannin na kwata-fainal zagaye-biyu (gida da waje), inda waɗanda suka yi nasara za su tsallaka zuwa wasannin dab da ƙarshe a babbar gasar ƙungiyoyin Afirka.

A cewar jadawalin gasar da aka fayyace a lokacin canke a Cairo a watan da ya gabata, wanda ya ci wasa tsakanin Espérance da Al Ahly zai fuskanci ƙungiyar da ta ci wasa tsakanin Mamelodi Sundowns da Stade Malien.

A ɗayan gefen kuwa, wanda ya yi nasara tsakanin AS FAR da Pyramids FC zai haɗu da wanda ya ci wasa tsakanin RS Berkane da Al Hilal.

An tsara wasannin dab-da-na-ƙarshe a Afrilu, inda za a buga wasannin farko tsakanin 10 da 12 na Afrilu, da wasannin ramuwa tsakanin 17 da 19 ga Afrilu.

Wasan ƙarshe mai zagaye-biyu za a buga shi a watan Mayu domin tantance sabon zakaran ƙungiyoyin Afirka.