Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran, IRGC ta sanar da kama aƙalla mutum 127 a sassa daban-daban na ƙasar, inda ta ce suna da alaƙa da Birtaniya da Amurka da kuma Isra’ila, kuma suna “taya abokan gaba shirya yadda za a kai harin soji ta ƙasa.”
A cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim, an kama mutum bakwai a lardin Gabashin Azerbaijan, inda aka zarge su da “shirya makamai da tsara ayyukan ɓarna, tare da aika bayanan wurare masu muhimmanci ga abokan hulɗarsu a ƙasashen waje.”
Haka kuma, an kama mutum 69 a lardin Mazandaran, yayin da aka gano wasu 51, ciki har da ƙungiyoyin leƙen asiri uku a lardin Kerman.
Tehran ta tsare mutane da dama kan zargin leƙen asiri tun bayan yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 3,000.
Sabuwar dokar leƙen asiri da aka ƙarfafa a Iran na bai wa hukumomi damar yanke hukuncin kisa ga waɗanda aka samu da laifin leƙen asiri, tare da ƙwace dukiyoyinsu.









