| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
Sifaniya da Maroko suna zazzafar fafutuka don zama masu masaukin babban wasa, duk da cewa har yanzu FIFA ba ta sanar da inda za a yi ba.
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
HOTON TARIHI: Wani hoto na gaba ɗaya da ke nuna aikin gina Filin Wasa na Hassan II a Benslimane, kusa da Casablanca

Rahotanni daga maroko na cewa Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Morocco (RMFF), na cewa za a gudanar da wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2030 a birnin Casablanca.

Kamfanin yaɗa labarai ta Sifaniya EFE ce ta sanar da haka ranar Alhamis.

Duk da cewa har zuwa yanzu hukumar ƙwallo ƙafa ta duniya, FIFA ba ta sanar da wajen da za a gudanar da wasan karshe na babbar gasar da za a yi a 2030 ba, Sifaniya da Maroko ne ke taƙaddama kan batun.

Kamfanin EFE ya ambato shugaban RMFF, Fouzi Lekjaa yana faɗin haka yayin wani taron jam'iyyar siyasa a garin Bouznika na Maroko a ranar Alhamis.

'Lardin Benslimane zai samu alfarmar zama masaukin wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta 2030,' cewar Lekjaa.

Sai dai kuma wata sanarwa daga kakakin FIFa ta ce, 'FIFA za ta yanke shawara a lokacin da ya dace.'

Haka nan kamfanin Reuters ya tuntuɓi hukumar ƙwallo ta Maroko, RMFF da kuma ta Sifaniya, RFEF domin neman ƙarin bayani.

Gina sitadiyom

Benslimane birni ne da ke da nisan kilomita 60 daga Casablanca, kuma shi ne wurin da ake gina filin wasa na Hassan II, da ya kai tsadar dala biliyan 1, wanda ake gina shi don Gasar Kofin Duniya.

Ana sa ran filin zai ɗauki kujerun zama kimanin 115,000, kuma zai zama mafi girman filin wasa da aka yi musamman don ƙwallon ƙafa a duniya.

Gasar Kofin Duniya mai zuwa za ta kasance ta musamman, inda za a gudanar da wasanni a ƙasashe shida a nahiyoyi uku a karo na farko.

Duk da cewa wasannin buɗe gasar guda uku za su gudana a Argentina, Paraguay, da Uruguay, yawancin gasar za ta gudanar a Maroko, Portugal, da Sifaniya.

FIFA ba ta kammala zaɓen dukkan biranen da za su zama masauki wasannin ba tukuna. Amma Maroko da Sifaniya na son samun wasan ƙarshe.

A baya ba a sanar da wurin wasan ƙarshe na Gasar FIFA 2026 ba sai a watan Fabrairun 2024. Amma a farkon watan nan, an ambato shugaban RFEF, Rafael Louzan yana cewa 'Sifaniya ce ya kamata ta karɓi wasan ƙarshe'.

Haka nan FIFA ta faɗa a watan Agusta cewa rahotannin kafafen watsa labarai da ke iƙirarin cewa Shugaban FIFA, Gianni Infantino ya yi alƙawarin ba wa Maroko wasan ƙarshe ‘ba gaskiya’ ba ne.