Tawagar ƙwallon ƙafar Jamhuriyar Nijar, Mena, ta yi sabon koci Nabil Neghiz, mai shekara 58, ɗan ƙasar Aljeriya.
A ranar Jumma’a ce aka yi bikin bayyana Neghiz a matsayin sabon kocin na tawagar ƙwallon ƙafar ta Nijar bayan tafiyar Badou Zaki, ɗan ƙasar Maroko.
Naɗin na koci ɗan Aljeriyar na zuwa a wani muhimmin lokaci ga tawagar ƙwallon ƙafar Nijar wadda ke ƙoƙarin komawa Gasar Kofin Afirka (AFCON), tun bayan ta samu damar shiga gasar a shekarar 2013.
Saboda haka, muhimmin aikin Neghiz zai kasance ya taimaka wa Mena domin samun gurbin zuwa gasar AFCON ta shekarar 2027 tare da gina wata tawaga mai ƙarfi da za ta iya kare martabar Nijar a nahiyar, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP.
Koci mai shekara 58 mai tarihin ƙwarewa a aiki
An haifi Nabil Neghiz ranar 25 ga watan Satumba na shekarar 1967 a Jijel, Algeriya, kuma ya yi karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ƙasar inda ya ƙware a kan harkar ƙwallon ƙafa.
Ya shafe shekaru yana aiki a matsayin koci a matakin kulob da na ƙasa.
Ya fara aikin kocinsa ne a ƙananan ƙungiyoyin Aljeriya da suka haɗa da Mouloudia de Kaous, wadda ya taimaka ta kai matakin lig na uku a kakar 2006-2007.
Kana ya jagoranci ƙungiyar Entente de Collo, wadda ya kai mataki na gaba, kafin ya ci gaba da aikinsa a MO Constantine a matsayin mataimakin koci.
Kazalika lokacin jagorancinsa a CRB Aïn Fakroun wani muhimmin lokaci ne a tarihin aikinsa.
A ƙarƙashin jagorancinsa, ƙungiyar ta samu ci-gaba sau biyu a jere, inda ta koma matakin babbar gasar lig ɗin Aljeriya.
Daga nan ne ya koma aikin kociya a WA Tlemcen kana ya koma Olympique de Médéa.
Aikinsa na farko a matakin tawaga ta ƙasa
Sai dai kuma a tawagar ƙwallon ƙafar Aljeriya ne Nabil Neghiz ya fara aiki da tawaga ta ƙasa.
A shekarar 2014, shiga cikin jami’an kociya na tawagar Fennecs ta Aljeriya a matsayin mataimaki ga koci Christian Gourcuff, ɗan Faransa.
Kana ya yi aiki da Milovan Rajevac, lamarin da ya sa ya yi aikin kociya ga tawagar ƙwallon ƙafa ta Aljeriya wadda ke shiga muhimmiyar gasar Afirka.
A shekarar 2016, bayan tafiyar Christian Gourcuff, an bai wa Neghiz kocin riƙo na tawagar ƙwallon ƙafar Aljeriya.
A muhimmin wasansa na farko a matsayin kocin Fennecs, tawagar ta Aljeriya ta doke Seychelles 2-0 ranar 2 ga watan Yuni na shekarar 2016, wani sakamako da ya bai wa Aljeriya damar shiga Gasar Kofin Afirka ta 2017.
Shiga Gasar Kofin Afirka da shirya ‘yanwasan da ke taka leda a lig daban-daban na cikin muhimman abubuwa a tarihin ƙwarewar da kocin ya shigo da su tawagar Nijar, in ji ANP.
Shin kocin na Aljeriya zai iya kai tawagar Nijar Gasar Kofin Afirka ta 2027?
A cikin watan Satumban nan ne dai za a fara wasannin neman shiga gasar.
Nijar tana cikin rukunin A ne wadda ke da tawagogin ƙasashen da suka haɗa da Maroko da Gabon da Lesotho da Nijar.
Nijar za ta buga wasanta na farko ne da tawagar Lesotho ranar 25 ga watan Satumba.















