| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Real Madrid na shirin ɗauko Allegri don maye gurbin Arbeloa
Yayin da kocin Real Madrid Alvaro Arbeloa ke shan suka saboda raguwar tagomashin ƙungiyar, rahotanni na cewa mahukuntan kulob ɗin sun fara shirin maye gurbinsa.
Real Madrid na shirin ɗauko Allegri don maye gurbin Arbeloa
Real Madrid na shirin ɗauko Allegri don maye gurbin Arbeloa / Others
6 awanni baya

Kocin Real Madrid, Alvaro Arbeloa ya fara samun matsin-lamba yayin da ƙungiyar ta fara rasa tagomashin da ta samu tun bayan da ya karɓi ragama daga hannun Xabi Alonso.

Hasali ma, rahotannin na cewa tuni shugaban Real Madrid, Florentino Perez ya fara baza komar neman wanda zai maye gurbin Arbeloa.

Arbeloa ya samu babbar suka bayan rashin nasarar da Madrid ta yi a hannun Getafe da ci 0-1, wanda ya janyo Barcelona ta kere musu da maki huɗu a teburin La Liga.

Baya ga dukan da suka sha, wasan ya bayyana raunin haɗin-kai tsakanin ‘yanwasan Real Madrid, da rashin ɗa’a, da kuma rashin tabbas a ƙoƙarinsu.

A wasan wanda a gida Madrid ta buga shi, ɗanwasanta na baya Franco Mastantuono ya samu jan kati kai-tsaye a minti 5 na ƙarin lokaci a ƙarshen wasan.

A halin yanzu, babban abin damuwa a zukatan masoya Madrid shi ne yadda Arbeloa zai kai su gaci a gasar Zakarun Turai da za a ci gaba da bugawa mako mai zuwa, musaamman ganin an shiga zagayen ‘yan-16.

Martanin Allegri

Alamu na nuna cewa shugabanni a Madrid ba su gamsu da kamun ludayin matashin koci Alvaro Arbeloa ba, don haka suka fara duba yiwuwar ɗauko kocin AC Milan, Massimiliano Allegri don jan ragamar ƙungiyar a kakar 2026-27.

Sai dai kuma a ɓangarensa, Allegri na da kwantiragi a AC Milan ta Italiya, wadda za ta kai shekarar 2027, duk da cewa ba kasafai masu horarwa ke ƙin karɓar tayin horar da babban kulob irin Real Madrid ba.

A tarihi, ba wannan ne karon farko da Allegri ke samun tayi daga Real Madrid ba. Sau biyu Madrid tana yunƙurin ɗauko shi, a 2019 da 2021 amma abin bai tabbata ba.

Sai dai a baya-bayan nan, an ambato Allegri yana mai da martani kan yiwuwar barin Milan, inda ya jaddada cewa babu matsala tsakaninsa da shugabannin ƙungiyar.