Taƙaddama a kan gyaran dokar zaɓe ta Nijeriya

Sai dai, babban abin da ya tada kura shi ne matakin da Majalisar Dattawa ta dauka na cire wani sashi mai muhimmanci a cikin dokar.

By
Shugaban Majalisar Dinkin Najeriya - Godswill Akpabio / Others

Wani batu da yake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya a fagen siyasar Nijeriya shi ne batun gyaran Dokar Zabe ta shekarar 2022. 'Yan Nijeriya da dama na fatan wannan gyara zai magance kura-kuran da aka samu a zabukan 2023.

Sai dai, babban abin da ya tada kura shi ne matakin da Majalisar Dattawa ta dauka na cire wani sashi mai muhimmanci a cikin dokar.

Babban abin da ya raba kawunan masu ruwa da tsaki shi ne batun wajabta aikawa da sakamakon zabe kai-tsaye ta intanet (electronic transmission).

Yayin da Majalisar Wakilai ta amince da sanya hakan a matsayin "tilas", ita kuwa Majalisar Dattawa ta dage kan cewa hakan "zabi ne", ba wajibi ba.

Wannan matsayar ta Majalisar Dattawa ta sa Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) gudanar da zanga-zanga a gaban Majalisar Dokoki da ke Abuja a ranar Litinin, domin matsa lamba ga sanatocin su sauya matsayarsu.

Masu fafutika na ganin cewa ƙin wajabta aikawa da sakamakon zaben zai rage kwarin gwiwar jama'a kan sahihancin zaben 2027.

Suna zargin cewa barin batun a matsayin "zabi" zai iya zama wata kafa ta tafka maguɗi, musamman a matakan tattara sakamako (collation centers) inda aka saba samun matsaloli.

An kwashe shekaru masu yawa ana yin zaɓuka a Nijeriya, sai dai galibi zarge-zargen magudi suna dabaibaye tsarin ne musamman a lokacin tattara sakamako.

A mafi yawan lokuta, mutane suna kaɗa ƙuri’unsu ne cikin lumana a rumfunan zaɓe, amma matsalar tana farawa ne lokacin aikawa da sakamakon daga wata cibiyar tattara sakamakon zuwa wata.

A wannan gaɓar ne ake zargin ana samun sauya alkaluma ko ɓatan sakamako na gaskiya.
Hakan ce ta sa a ƙoƙarin magance magudi kafin zaɓukan 2023, Hukumar INEC ta gabatar da na'urar BVAS da shafin IReV.

Tsarin IReV (INEC Result Viewing Portal) wani babban shafin intanet ne da aka samar domin:

Dakile aringizon kuri'u.

Inganta gaskiya da amana.

Wallafa hoton takardar sakamakon zaɓe (Form EC8A) kai-tsaye daga rumfar zaɓe.

Bai wa kowane ɗan ƙasa damar ganin sakamakon kowace rumfa ta wayarsa ko kwamfuta a duk inda yake.

Tabbatar da cewa abin da aka bayyana a rumfar zaɓe, shi ne abin da zai je babban shafin hukumar ba tare da an sauya shi a hanya ba.

Manufar ita ce: da zarar an kammala ƙidaya ƙuri'u a rumfar zabe, jami'ai za su tura sakamakon kai-tsaye zuwa shafin intanet domin kowa ya gani.

Duk da cewa Majalisar Dattawa ta tafi hutun mako biyu bayan amincewa da dokar a makon jiya, shugabancin majalisar ya kira wani taron gaggawa a ranar Talata.

Kodayake ba a bayyana dalilin taron ba, ana kyautata zaton za a sake nazarin wannan sashi na aikawa da sakamako ne sakamakon matsin lamba daga jama'a.

Masana na nan akan bakarsu cewa: muddin aka wajabta tura sakamako daga rumfunan zabe zuwa shafin IReV, za a rage kura-kuran da suka dabaibaye harkar zabe a Nijeriya tsawon shekaru.