An samu rahotanni 32 na yi wa 'yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher - Likitoci

Wasu daga cikin 'yan matan an yi musu fyaɗe a cikin Al Fasher bayan RSF ta ƙwace garin, yayin da wasu aka ci zarafin su a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa zuwa garin Tawila da ke maƙwabtaka, in ji Ƙungiyar Likitocin Sudan.

By
Yaƙin na Sudan tsakanin sojoji da RSF, wanda ya fara a Afrilun 2023, ya kashe aƙalla mutum 40,000 kuma ya tilasta wa mutane miliyan 12 barin gidajensu

Wata ƙungiyar likitoci ta Sudan ta bayar da rahoton fyaɗe 32 da aka yi wa ‘yan matan da ke tserewa daga Al Fasher cikin mako guda, a daidai lokacin da birnin da ke yammacin na Sudan ke ci gaba da kasancewa a hannun hannun mayaƙan ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF).

Wasu daga cikin 'yan matan an yi musu fyaɗe a cikin Al Fasher bayan RSF ta ƙwace garin, yayin da wasu aka ci zarafin su a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa zuwa garin Tawila da ke maƙwabtaka, in ji Ƙungiyar Likitocin Sudan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.

Ta yi Allah wadai da fyaɗen a matsayin "ƙeta alfarmar ta ƙasa da ƙasa kuma yana daidai da laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama."

Sanarwar ta ce waɗannan laifuka "suna bayyana yadda rashin tsari da cin zarafi yake shafar mata da 'yan mata a wuraren da RSF ke iƙirarin iko da su, a cikin yanayin da babu kariya kuma babu wani nau'i na sa ido."

Ƙungiyar likitocin ta ɗora cikakken alhakin ga RSF kuma ta yi kira na gaggawa da a gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa mai zaman kansa da samar da kariya nan take ga waɗanda abin ya shafa da shaidu da kuma bai wa ƙungiyoyin lafiya da na jinƙai damar shiga ba tare da takunkumi ba don samar da kulawa, magani, da shawarwarin natsar da ƙwaƙwalwa da na shari'a.

Yaƙin na Sudan tsakanin sojoji da RSF, wanda ya fara a Afrilun 2023, ya kashe aƙalla mutum 40,000 kuma ya tilasta wa mutane miliyan 12 barin gidajensu, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

A watan da ya gabata, RSF ta ƙwace Al Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa, inda ake zarginta da kai hare-hare da kisan kiyashi. Kungiyar tana da iko da duka jihohin Darfur guda biyar a cikin jihohin Sudan 18, yayin da sojoji ke rike da mafi yawan sauran jihohin 13, ciki har da Khartoum.

Darfur ita ce kusan kusan ɗaya bisa biyar na yankin Sudan, amma mafi yawan mutanen ƙasar kimanin miliyan 50 suna rayuwa a yankunan da sojoji ke mulki.