Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shirin aron kuɗi daga ƙetare da ya kai dala biliyan 21 a harkar kasafin kudin shekarar 2025 zuwa 2026.
Wannan ya biyo bayan ba’asi da kuma amincewa da suka yi da rahoton kwamitin majalisar kan bashi na cikin gida da na ƙetare, wanda shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wamakko (mai wakiltar Sokoto ta Arewa) ya gabatar .
Cikakken shirin aron kuɗin ya ƙunshi dala biliyan 21.19bn na aron da ba na kai-tsaye ba da fam biliyan 4bn da Yuan biliyan 15bn da tallafin dala miliyan 65 da kuma aron kuɗaɗe daga cikin gida ta hanyar takardun lamuni.
Har wa yau shirin ya ƙunshi tanadi na samar da dala biliyan biyu ta hanyar takardun lamuni na kuɗaɗen ƙetare a kasuwar cikin gida.
Muhimman ɓangarorin da shirin rancen ya mayar da hankali a kai sun haɗa da ababen more rayuwa da fannin noma da tsaro da makamashi da gidaje da kuma sadarwa na intanet.
Ɗaya daga cikin muhimman ɓangarorin shi ne dala biliyan uku da za a kashe wajen farfaɗo da layin dogo na gabashin ƙasar, kama daga birnin Port Harcourt zuwa Maiduguri.
A jawabinsa, Wamakko ya ce an gabatar da shirin ne ga Majalisar Dokokin ƙasar ranar 27 ga watan Mayu, amma an jinkirta shi domin hutun da majalisar ta tafi da kuma harhaɗa bayanai a ofishin lamuni na Nijeriya.
A bayaninsa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin (mai wakiltar arewacin Kano), ya ce shirin aron ya mayar da hankali kan haɗa kan ƙasa.










