Sudan ta sake buɗe filin jiragen sama na Khartoum bayan yaƙin kusan shekaru uku
Jirgin kamfanin jiragen saman Sudan ya sauka a filin jirgin saman Khartoum daga birnin Port Sudan ranar Lahadi, a wani mataki na sake dawowa da sufuri sama baya kusan shekaru biyu da yaƙi ya ɓarke .
Sudan ta fara jigilar matafiya a cikin ƙasar zuwa filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Khartoum a karon farko tun bayan yaƙi ya ɓarke da rundunar RSF a watan Afrilun shekarar 2023, inda wani jirgin kamfanin jiragen sama ya iso daga Port Sudan, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar ta ruwaito.
Jirgin, na kamfanin jiragen saman Sudan ɗauke da matafiya fararen-hula, ya sauka a filin jiragen saman Khartoum bayan kusan shekaru biyu da dakatar da aiki sakamakon yaƙi tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar SUNA.
Jigilar ta nuna jajircewar kamfanin jiragen saman Sudan kan nauyin da ya rataya a wuyansa wajen tallafa wa sufurin sama, sake haɗa biranen Sudan da kuma sauƙaƙa matsalolin tafiye-tafiye da ‘yan ƙasar ke fuskanta tun lokacin da aka fara yaƙi , in ji SUNA .
Kamfanin dillancin labaran ya bayyana matakin a matsayin “muhimmin ci-gaba ” wajen dawo da jigilar matafiya zuwa filin jiragen sama na Khartoum da kuma wata manuniya ga sabon mataki na farfaɗo da zaman lafiya , inda rayuwa ke komawa babban birnin ƙasar sannu a hankali.
A watan Oktoban da ya gabata, hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama na fararen-hula a Sudan ta yi shelar shirin sake buɗe filin jiragen saman, amma an kai wa filin hare-hare ta jirage mara matuƙa . Rundunar sojin Sudan ta bayyana wancan lokacin cewa ta tare jirage mara mata da RSF ta tura filin jiragen saman.
Rufe filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Khartoum, babbar cibiyar sufurin sama ta Sudan, ya katse jigilar matafiya ta sama a faɗin ƙasar sosai domin kasancewarta a tsakiyar ƙasar da kuma girmanta.