| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta kashe sojojin Amurka biyu, yayin da Trump ya ba da umarnin kai mata hare-hare
Shugaba Donald Trump ya bayyana mace-macen a matsayin "abun matuƙar baƙin ciki," yana mai bayyana cewa shi ya tsani ganin hakan na faruwa.
Iran ta kashe sojojin Amurka biyu, yayin da Trump ya ba da umarnin kai mata hare-hare
TSOHON HOTO: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi ya tsani ganin hakan na faruwa

Hare-haren makamai masu linzami da jirage mara matuƙa na Iran sun kashe akalla sojojin Amurka biyu tare da ɓatar da wani sojin Amurkan a ƙasar Jordan.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na X, hedikwatar tsaron Amurka (CENTCOM) ta tabbatar da cewa wannan lamarin ya auku ne ranar 17 ga watan Yuli yayin da dakarun Amurka da na Jordan ke famar daƙile hare-haren Iran.

Kazalika saƙon ya ƙara da cewa an garzaya da sojojin Amurka huɗu asibitocin ƙasar Jordan, tana mai ƙarawa da cewa tuni aka sallami sojojin daga asibitocin.

Saƙon kuma ya ce waɗanda aka tatbbatar cewa ba su ji rauni da yawa ba sun koma bakin aiki.

"Saboda girmamawa ga iyalan [waɗanda lamarin ya shafa], CENTCOM za ta riƙe ƙarin bayani, ciki har da sunayen gwarzayen da suka rasu, har zuwa bayan sa’o’i 24 bayan an sanar da ‘yan ‘yanuwansu ," in ji hedikwatar tsaron..

Shugaba Donald Trump ya bayyana mace-macen a matsayin "abun matuƙar baƙin ciki ."

"Mun tsani ganin hakan ya faru. Hidima ce ga ƙasarmu," kamar yadda ya shaida wa NewsNation.

‘Hukunta’ Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran

Sai dai kuma Amurka ta ƙaddamar da wani sabon jerin hare-haren sama kan Iran bayan hare-harenta sun kashe sojojin Amurkan biyu a Jordan, in ji sojin na Amurka.

Hedikwatar tsaro ta Amurka (CENTCOM) ta ce ta fara kai hare-haren ne ranar Asabar a ƙarƙashin umarnin Shugaba Donald Trump.

"A yau da misalin ƙarfe 6 na yamma agogon ET, dakarun Amurka sun fara ƙaddamar da hare-haren sama kan Iran ƙarƙashin umarnin babban kwamandan ƙasa. An tsara hare-haren da niyyar sake kassara ikon Iran na iya barazana ga jigilar kayyaykin kasuwanci a mashigar Hormuz da gagauta hukunta Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran da ta ƙaddamar da hare-hare kan sojojin Amurka a Jordan jiya da daddare," in ji saƙon da CENTCOM ta wallafa a shafin X.