NIJERIYA
2 minti karatu
An kashe ‘yan ta’adda 24 cikin kwana shida a Nijeriya - Rundunar Soji
An gudanar da waɗannan ayyuka ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli a Dajin Sambisa, da Dandalin Timbuktu da kuma Tsaunukan Mandara da ma wasu wuraren daban.
An kashe ‘yan ta’adda 24 cikin kwana shida a Nijeriya - Rundunar Soji
Sojojin Nijeriya
10 Yuli 2025

Haɗakar dakarun Operation Hadin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 24 a wasu sabbin hare-hare da suka ƙaddamar a maɓoyar ‘yan ta’addan a yankunan daban-daban a arewa maso gabashin Nijeriya.

Kwamandan haɗakar rundunar Operation Hadin Kai a Arewa Maso Gabas, Janar Abdulsalam Abubakar ya ce an kai samamen ne bayan tattara bayanan sirri, inda ya ce an kuma kashe mutum biyar da suke samar wa ‘yan ta’addan kayayyakin amfani, a wani kwanton ɓauna da aka yi musu da daddare.

An gudanar da waɗannan ayyuka ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli a Dajin Sambisa, da Dandalin Timbuktu da kuma Tsaunukan Mandara da ma wasu wuraren daban.

A yayin samamen, rundunar ta ce an yi nasarar ƙwato muggan makamai da dama da babura da kekuna da kayan abinci da kuma kaki da takalman sojoji.

Manjo Janar Abdulsalam ya ce rundunar hadin gwiwa ta bangaren sojin sama, da Civilian Joint Task Force, da na sojojin Najeriya ne suka gudanar da aikin.

Shi ma Kakakin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ Kyaftin Reuben Kovangiya, ya bayar da cikakken bayanin ayyukan a cikin wata sanarwa.

A ci gaba da gudanar da jerin hare-hare na hadin gwiwa a fadin Arewa maso Gabas, sojojin  Operation HADIN KAI (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunonin sojin sama da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force da mafarauta, sun yi nasarar gudanar da samame a kan 'yan ta'addar Boko Haram/ISWAP daga tsakanin 4 - 9 ga Yulin 2025 inda suka kawar da ‘yan ta’adda da dama.

A daya daga cikin samamen da aka kai a Platari a ranar 4 ga watan Yulin 2025, yayin da sojojin suka yi kwanton ɓauna, sun far wa ‘yan ta’addar JAS/ISWAP da ke kan babura da ke tafiya daga dajin Sambisa zuwa Dandalin Timbuktu.

Nan take aka fatattaki ‘yan ta’addan ta hanyar buɗe musu wuta, lamarin da ya kai ga halaka ‘yan ta’adda 3.

Hakazalika, bayan samun bayanan sirri kan zirga-zirgar 'yan tada kayar bayan a kewayen yankin Komala, sojoji sun sake yi wa 'yan ta'adda kwanton ɓauna, inda suka kashe wani mayakin.

 

 

Rumbun Labarai
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da kisan Kiristoci - Sheik Bala Lau
China na adawa da Trump kan amfani da 'addini da ‘yancin ɗan'adam' domin tsoma baki a Nijeriya
Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar
Jami'an tsaron Nijeriya sun hallaka 'yan bindiga 19 a Jihar Kano
Yadda barazanar da Trump ya yi kan aika sojoji Nijeriya ta tayar da ƙura
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su Jihar Kogi
Ya kamata Amurka ta taimaka wa Nijeriya da makamai maimakon barazana —Kwankwaso
Muna shirin ɗaukar mataki kan Nijeriya - Sakataren Ma’aikatar Yaƙi na Amurka
Trump ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta Amurka ta soma shirin yiwuwar kai hari Nijeriya
Tinubu ya mayar da martani bayan Amurka ta ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta sake jaddada aniyarta ta yaƙi da tsattsauran ra'ayi
Samaila Bagudo: 'Yan bindiga sun sace Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kebbi
Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla
‘Yan sandan Nijeriya sun ceto ‘yan kasashen waje 23 da aka yi garkuwa da su
An yi gagarumin garambawul ga rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya
EFCC ta tilasta wa boka dawo da gidaje da motocin da ya damfari wani mutum a Nijeriya
Tinubu ya amince da harajin kashi 15 cikin 100 kan man fetur da gas da ake shigarwa ƙasar