| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Sanƙarau ta kashe mutum 33 a Sokoto yayin da hukumomi ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta
Gwamnatin jihar ta ce an samu aƙalla mutum 256 da cutar ta kama a fadin ƙananan hukumomi takwas na jihar tun bayan sake ɓullarta kimanin wata ɗaya da ya gabata.
Sanƙarau ta kashe mutum 33 a Sokoto yayin da hukumomi ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta
Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu / Others

Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar ƙananan yara 33 bayan sake ɓullawar cutar sanƙarau a sassan jihar, yayin da hukumomin lafiya ke fama da ƙaruwar yaɗuwar cutar .

Da yake tabbatar da bullar cutar, kwamishinan lafiyar jihar, Dakta Faruk Abubakar, shi ya bayyana wannan a lokacin wani taron wayar da kan jama’a da hakimai .

Hukumar inganta lafiya a matakin farko ta jihar ce ta shirya taron da haɗin gwiwar ƙungiyar Sightsavers da gidauniyar Chigari Foundation.

Kwamishinan ya ce: “an samu aƙalla mutum 256 da suka kamu da cutar a fadin ƙananan hukumomi takwas na jihar tun lokacin da cutar ta sake ɓullowa kimanin wata ɗaya da ya wuce.

“Sabon Birni ce ta samu mutane mafi yawa da suka kamu da cutar inda mutum 63 suka kamu da ita, sannan sai Wamakko da mutum 60, da Shagari da mutum 51, da Tambuwal da mutum 33, da kuma Dange Shuni da mutum 26.

Kebbi ta ba da rahoton kamuwar mutum 16 da cutar, yayin da Bodinga da Gada da Kware suka samu mutum biyu da mutum ɗaya da kuma mutum biyu.”

Dakta Abubakar ya ce yawancin mace-macen sun faru ne cikin jama’a kafin a kai mutane asibiti, yana mai ɗaura laifin kan jinkirta ba da magani da kuma tunanin cewa matsala ce ta sihiri maimakon abin da ke buƙatar taimakon gaggawa na asibiti.

Alamun cutar sanƙarau ɗin sun haɗa da zazzaɓi na ba-zata da ciwon kai mai tsanani da kafewar wuya da amai da ɗimuwa da ƙin haske da rawan jiki.

Ƙwararru a fagen lafiya suna gargaɗin cewa idan ba a yi magana ta gaggawa ba, cutar za ta iya haddasa mutuwa cikin sa’o’i ko kuma ta janyo tawaya ta dindindin kamar rasa ji da lalata ƙwaƙwalwa ko kuma shanyewar jiki.

Domin daƙile yaɗuwar cutar, gwamtin jihar, da hadin gwiwar ƙungiyar ba da agaji ta likitocin duniya Médecins Sans Frontières, sun kafa wani sansani na killace mutane a manyan asibitocin da ke Dogon Daji da Tambuwal, inda aka ware wuraren ajiye marasa lafiya mata daban da na ajiye maza daban.

Kwamishinan ya ƙara da cewa duk da cewa gwaje-gwaje 20 kawai ne suka tabbatar da cutar cikin waɗanda aka gwada kawo yanzu, mara lafiya da aka kawo da wuri suna samun sauƙi kuma ba a samu wata mutuwa ba tun da hukumomi suka zafafa ɗaukar mataki.

Hukumomi sun ci gaba da kira ga mazauna yankin da su nemi taimako na gaggawa a asibiti idan suka ga wata alama ta cutar da kuma yin biris da wasu aƙidu na ƙarya da ake yaɗawa game da cutar, yayin da ake zafafa ƙoƙarin shawo kan cutar.