| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Sabon Firaministan Birtaniya Burnham ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa
Da yake jawabi a wajen ofishin Firaminista da ke 10 Downing Street a ranar Litinin, Burnham ya ce: "Birtaniya na bukatar ta nuna wa duniya cewa za ta iya dawo da kwanciyar hankalinta da zaman lafiyarta."
Sabon Firaministan Birtaniya Burnham ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa
Burnham da matarsa Marie-France van Heel sun dauki hoto a gaban gida mai lamba 10 Dawning Street

Sabon Firaministan Birtaniya Andy Burnham ya yi alƙawarin gabatar da sabbin matakai a wannan makon domin rage tsadar rayuwa, kafin daga bisani ya bayyana wani sabon shirin gyaran ƙasar na tsawon shekaru 10 daga baya a wannan shekara.

Da yake jawabi a wajen ofishin Firaminista da ke 10 Downing Street a ranar Litinin, Burnham ya ce: "Birtaniya na bukatar ta nuna wa duniya cewa za ta iya dawo da kwanciyar hankalinta da zaman lafiyarta."

Ya ƙara da cewa: "Ba mu yi abin da ya kamata ba, kuma dole ne mu fi haka." Yana mai yi wa 'yan Birtaniya alƙawarin samun "ɗan sassauci a yanzu," Burnham ya ce gwamnatinsa za ta bayyana matakan da za ta ɗauka domin rage tsadar rayuwa, tare da yadda za ta samar da kuɗin aiwatar da su.

Game da shirye-shiryen dogon lokaci kuwa, ya ce: "Za mu taimaka wa matasa da dama su samu aikin yi ta hanyar sauya tsarin ilimi da ƙara musu tallafi, ciki har da tallafin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa. Haka kuma za mu gina ƙarin gidajen gwamnati masu araha."

"Wannan ita ce hanya mafi adalci kuma mafi ɗorewa ta rage kuɗaɗen jin daɗin al'umma, tare da bin ƙa'idojinmu na kasafin kuɗi da kuma cika alƙawuranmu na tsaro ga ƙawayenmu na ƙasa da ƙasa," in ji Burnham.

Tun da farko, Fadar Buckingham ta tabbatar da cewa Andy Burnham ya zama sabon Firaministan Birtaniya.

Burnham ya isa Fadar Buckingham jim kaɗan bayan Keir Starmer ya miƙa takardar murabus dinsa a hukumance daga mukamin firaminista.

A yayin ganawarsa da Sarki Charles na Uku, an bukaci Burnham ya kafa sabuwar gwamnati, wanda hakan ya tabbatar da shi a matsayin sabon firaministan ƙasar.

Kafin hakan, Starmer ya gabatar da jawabinsa na ƙarshe a matsayin firaminista a gaban ofishin 10 Downing Street, inda ya ce:

"Aikina ya ƙare."

Ya kuma yi wa magajinsa, Andy Burnham, fatan samun nasara, tare da gode wa ma'aikatan 10 Downing Street da matarsa, Victoria, bisa goyon bayan da suka ba shi.

A cikin wata sanarwa, Fadar Buckingham ta ce:

"Sir Keir Starmer, ɗan Majalisar Dokoki, ya gana da Mai Martaba Sarki da safiyar yau, inda ya miƙa takardar murabus dinsa daga mukamin Firaminista da kuma Babban Sakataren Baitulmali, wanda Mai Martaba ya amince da ita."

Ana sa ran Burnham zai isa 10 Downing Street daga baya a ranar Litinin domin gabatar da jawabinsa na farko a matsayin Firaministan Birtaniya.