| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Gwamnatin Ghana ta kashe $4.37m don kwashe 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu
Gwamnatin Ghana ta kashe $4.37m don kwashe 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu
Bayan rikicin kyamar yan ci rani a Afirka ta Kudu, Ghana ta kwashe dubunnan jama'arta daga kasar.

Gwamnatin Ghana ta sanar da kashe kimanin Cedi miliyan 49,721,786 kwatankwacin $4.37m don kwashe 'yan kasarta daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren ƙyamar baƙi da aka fuskanta a ƙasar.

Aikin kwashe ‘yan ƙasar ta Ghana da aka gudanar a tsakanin 24 ga Mayu da 4 ga Satumban 2026, ya ƙunshi jigila da jiragen sama na fasinjoji na shata da wajen kwana da abinci da kula da lafiya, a cewar gwamnatin ƙasar.

A yayin wata tattaunawa da manema labarai a babban birnin Accra ranar Litinin, Ministan Harkokin Wajen Ghana Samuek Okudzeto Ablakwa ya bayyana yawan kuɗaɗen da aka kashe a ayyukan kwashe ‘yan ƙasar Ghana daga Afirka ta Kudu.

Ya ce an kashe Cedi 38,835,152 wajen sayen tikiti da shatar jiragen sama na musamman, da wajen kwana da abinci da kula da lafiya.

Ministan ya ƙara da cewa an kashe wata Cedi miliyan 10,802,000 don sake shigar da mutanen cikin al’umma da biyan alawus ɗin tafiye-tafiye, yayin aka kuma kashe Cedi 84,274 don dawo da wasu gawarwakin ‘yan Ghana biyu zuwa gida bayan rasuwar su a Afirka ta Kudu.

Minista Ablakwa ya ƙara da cewa gwamnati ta biya dukkan kuɗaɗen da aka kashe, yayin da aka kuma bai wa kowane ɗan ƙasar ta Ghana da aka dawo da shi gida Cedi 5,500.

Kazalika ya ce an duba lafiyar dukkan waɗanda aka dawo da su zuwa gida, sannan an saya musu katin waya ɗauke da kuɗi da data a ciki.

Ministan ya kuma tunatar da cewa an samu hare-hare kan baƙi da ‘yan ci-rani a Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa suka ga dacewar kuɓutar da ‘yan ƙasarsu daga ƙasar.

Ƙasashe da dama dai sun kwashe jama’arsu daga Afirka ta Kudu, yayin da ita da kanta Afirka ta Kudu ta yi jigilar mayar da wasu zuwa ƙasashensu bayan rikicin na ƙyamar baƙi a ƙasar da a shekarun baya ta yi yaƙi da tsarin fifita farar-fata ‘yan tsiraru a kan baƙaƙen-fata.