Ambaliyar ruwa ta kashe aƙalla mutum 21 a yankin Safi na Maroko

Maroko na fama da ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya da ambaliya a yankin Atlas mai cike da tsaunuka, bayan an kwashe shekara bakwai ana fama da ƙarancin ruwan sama lamarin da ya sa aka kwashe duk ruwan da ke ma'ajiyar ruwa ta yankin.

By
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya tare da lalata gidaje da sauran gine-gine a kudancin Maroko da ke gaɓar teku ranar 31 ga Oktoban 2012 [FILE]. / Reuters

Ambaliyar ruwa da aka yi bayan saukar mamakon ruwan sama ta kashe aƙalla mutu 21 a yankin Safi da ke gaɓar tekun Atlantika mai nisan kilomita 330 a kudancin Rabat, babban birnin Maroko, a cewar hukumomin ƙasar.

Kazalika ambaliyar, wadda aka yi a ranar Lahadi, ta jikkata mutum 32 kuma an kai galibinsu asibiti, in ji wata sanarwa da hukumomi suka fitar.

Ruwan sama da aka sheƙa tsawon awa ɗaya ya haddasa ambaliya a gidaje da shaguna tare da toshe hanyoyi a Safi da yankunan da ke maƙotaka da shi, a yayin da ma’aikatan bayar da agajin gaggawa suke ci gaba da aiki domin ceto mutane, a cewar hukumomi.