Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa

Sojojin sun kakkaɓo jirgi maras matuƙin samfarin ƙasar China a lokacin da yake wucewa ta saman birnin inda rahotanni suka ce jirgin ya nufi yammacin El-Obeid domin kai hari kan wuraren soja da na farar-hula

By
Wannan rikici na Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma tilasta wa miliyoyin mutane guduwa daga gidajensu.

Sojojin Sudan sun harbo jirgin sama maras matuƙi da dakarun RSF suke sarrafawa a birnin El-Obeid a Jihar Kordofan ta Arewa a safiyar Asabar, kamar yadda watsa labarai na cikin gida suka ruwaito.

Shafin Sudan News, ya ruwaito majiyoyin soji inda suke cewa sojojin sun kakkaɓo jirgi maras matuƙin samfarin ƙasar China a lokacin da yake wucewa ta saman birnin. An ce jirgin ya yi ƙoƙarin kai hari kan wuraren soja da na farar-hula a yammacin El-Obeid.

‘Yan gwagwarmaya sun yaɗa bidiyo a kafafen sada zumunta a lokacin da aka harbo jirgin, inda bayan an harbo shi jama’a suka yi ta ihu suna murna.

Babu wani bayani a halin yanzu game da jikkata ko wata ɓarnar daga harin da aka yi yunƙurin kaiwa.

Zugar jirage marasa matuƙa

RSF ta kai harin jiragen sama marasa matuki a ranar Juma'a, inda ta kai harin a wasu wurare a birnin Omdurman na Jihar Khartoum da kuma Atbara a Jihar River Nile, in ji wannan majiya.

A ranar Alhamis, sojojin Sudan sun ce makaman kariyarsu ta sama sun daƙile zugar jiragen sama marasa matuƙa da suka nufi Omdurman da ke yammacin Khartoum, da kuma garin Atbara a arewacin ƙasar.

Hukumomin Sudan sun zargi RSF da ƙara kai hare-hare ba iyaka da jiragen sama marasa matuƙa a kan farar-hula a Khartoum da sauran birane, ko da yake kungiyar ba ta mayar da martani a bainar jama'a kan tuhumar ba.

Tun daga 15 ga Afrilun 2023, sojojin Sudan da RSF suke yaƙi da juna inda har zuwa yanzu an kasa yin sulhu.

Wannan rikici na Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma tilasta wa miliyoyin mutane guduwa daga gidajensu.