Mutum biyu sun mutu a Ghana sanadin hatsarin jirgin sama

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya fara kamawa da wuta ne kafin ya faɗi a filin wasa na makarantar Oninku Drive School da ke Site 17, kusa da makarantar renon yara ta TMA Daycare a yankin Greater Accra na Ghana.

By
Toshon hoto na hatsarin jirgin saman dakon kaya na Nijeriya a Ghana a shekarar 2012 / Reuters

Mutane biyu ne suka mutu bayan da wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari sannan ya kama wuta kusa da filin wasa na wata makaranta a rukunin gidaje na ‘Tema Community One’ da ke yankin Greater Accra a Ghana a ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya fara kamawa da wuta ne kafin ya faɗi a filin wasa na makarantar Oninku Drive School da ke Site 17, kusa da makarantar renon yara ta TMA Daycare.

Bayanai sun ce jami’an rundunar ’yansandan ƙasar Ghana da na hukumar kwana-kwana ta ƙasar (GNFS) sun isa wurin cikin gaggawa domin kashe wutar da kuma tabbatar da tsaron yankin.

Babban jami’in hukumar kashe gobara, Ebenezer Yenzu, wanda shi ne jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a shiyyar Tema, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

“Mun samu kiran ne da misalin ƙarfe 12:59 na rana cewa gobara ta tashi a Community 1, Site 18. Bayan isarmu wurin, mun tarar da wata gagarumar gobara ta tashi sakamakon faɗuwar wani helikwafta kusa da katangar makarantar renon yara ta TMA Daycare,” in ji shi.

Ya bayyana cewa jami’an kashe gobara, tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Ghana (GHAPOHA), sun yi nasarar kashe wutar tare da killace yankin domin tabbatar da tsaro.

A cewar hukumar kashe gobara, an riga an fitar da malamai da ɗaliban da ke makarantar renon yara ta kusa da wurin kafin isar jami’an tsaron, abin da ya sa ba a samu asarar rayukan ba daga ɓangaren yaran.

Wasu mazauna yankin da suka garzaya wurin hatsarin sun shaida wa manema labarai cewa sun ga jirgin yana shawagi a sararin samaniya kafin su lura kwatsam yana faɗowa ƙasa.

Bincike 

Ana sa ran masu bincike za su fara kwashe tarkacen jirgin da ya yi hatsarin a Tema domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Kwamishinan hukumar binciken hatsarin jiragen sama, John M. K. Wumborti, ya bayyana cewa an riga an fara binciken share fage bayan da tawagar masu bincike ta ziyarci wurin a ranar Litinin.

Ya shaida wa manema labarai cewa jami’ai za su koma wurin a ranar Talata da safe domin fara tattara tarkacen jirgin don yin nazari dalla-dalla.