Hukumar NDLEA ta kama mutum 230 a samame daban-daban a Kano

An kai samamen ne a maɓoyar fitattun masu safarar ƙwayoyi a yankuna kamar su Kofar Ruwa, Tashar Rami, Rijiyar Lemo, Kurna, Mil Tara da sauran wurare da dama inda aka ƙwato tabar wiwi da sholisho da miyagun ƙwayoyi da makamai.

By
NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi da makamai a Kano

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) Reshen Jihar Kano ta ce ta kama mutane 230 da ake zargi tare da ƙwato adadi mai yawa na miyagun ƙwayoyi da makamai a lokacin wani samame na musamman na tsawon kwanaki 30 a da jami’an hukumar suka kai a faɗin Jihar Kano.

Kwamandan Tsare-Tsaren Hukumar, ACGN A.I. Ahmad ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Kano, kamar yadda gidan rediyon Nijeriya ya ruwaito.

Ya ce an gudanar da samamen ne tare da hadin gwiwar Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da Hukumar Tsaro ta Farar-Hula (NSCDC) da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya da Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya.

Ahmad ya bayyana cewa an kai samamen ne a kan maɓoyar fitattun masu safarar ƙwayoyi a yankuna kamar su Kofar Ruwa, Tashar Rami, Rijiyar Lemo, Kurna, Mil Tara, Zage, Dorayi Karshen Waya, Dawanau, Filin Idi, Research, Rimi Market, Zango, Kofar Mata, Kano Line da Ladanai.

Ya ce a lokacin samamen, jami’an sun kwato tabar wiwi da sholisho maganin tari mai codeine, sannan da makamai da dama waɗanda aka ƙera a cikin gida.

A cewarsa, wannan samamen ya rage yawan shaye-shaye da laifuffukan da suka shafi miyagun kwayoyi, ciki har da ta’addanci na matasa da ƙwacen wayoyi, inda ya ƙara da cewa al’umma sun fara jin tasirin hakan.

Ahmad ya yaba da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, yana mai cewa hadin gwiwar ya ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a jihar.

Ya jinjina wa jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, bisa yadda yake inganta hadin kai tsakanin hukumomi, tare da gode wa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kan rawar da ta taka ta hanyar bayanan sirri.

Haka kuma ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayanta wajen yaƙi da shaye-shaye da ta’addancin samari, yana mai cewa jajircewar gwamnati ta ƙarfafa ƙoƙarin tabbatar da tsaro da farfaɗo da masu fama da shaye-shaye.

Kwamandan ya yi kira ga shugabannin al’umma, iyaye, ƙungiyoyin farar-hula, da jama’a gaba ɗaya da su haɗa kai da hukumomin tsaro wajen yaƙi da shaye-shaye.