Afirka na fuskantar tarnaƙin bashin dala biliyan 90 a 2026, in ji S&P

Sai dai masana sun jaddada cewa wannan alama ce ta ɗorewar wasu muhimman ma’auni na bashi, ba wai ingantuwarsu sosai ba, domin gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da ke rage nauyin bashi na bukatar dogon lokaci.

By
Afirka na fuskantar tarnaƙin bashin dala biliyan 90 a 2026, in ji S&P / Reuters


Kamfanin S&P da ke bin diddigin basussukan duniya ta yi gargadi cewa gwamnatocin kasashen Afirka na fuskantar hadarin ƙaruwar bashi, yayin da jerin basussukan kuɗaɗen waje (kamar dala) da za su biya a shekarar 2026 ke ƙara matsin-lamba ga taskar ajiyar kudaden waje, lamarin da ke kara hadarin sake rance.

A sabon rahoton hangen nesa kan bashin gwamnatocin Afirka da hukumar ta fitar a ranar Litinin, an nuna cewa biyan bashin waje na gwamnatoci yanzu ya ninka fiye da sau uku idan aka kwatanta da shekarar 2012.

Benjamin Young na S&P ya rubuta a cikin rahoton cewa: “Yawan bashi mai tsanani da kuma karancin hanyoyin samun kudaden shiga za su ci gaba da zama babbar barazana. Kuma da yake ana sa ran biyan bashin waje na gwamnatoci zai wuce dala biliyan 90 a wannan shekara, matsalolin da suka shafi kudaden waje sun ƙaru.”

Ya kara da cewa: “Biyan bashin waje na gwamnatoci na kusantar kaiwa ƙololuwa.”
Masar ce ke da kusan kashi daya bisa uku na jimillar bashin da za a biya a wannan shekara, inda za ta biya kusan dala biliyan 27 na bashin uwar kudi. Bayan Masar, akwai Angola, Afirka ta Kudu, da kuma Nijeriya.

S&P ta ce matsakaicin kimar darajar bashi na kasashen yankin ya kai mafi girma tun karshen 2020, wanda hakan ke nuna ana samun gyare-gyare a manufofi da kuma ingantacciyar hanyar bunkasar tattalin arziki.

Sai dai masana sun jaddada cewa wannan alama ce ta ɗorewar wasu muhimman ma’auni na bashi, ba wai ingantuwarsu sosai ba, domin gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da ke rage nauyin bashi na bukatar dogon lokaci.

Saukin yanayin hada-hadar kudi a duniya da kuma sha’awar masu zuba jari na rarraba jarinsu sun bai wa wasu kasashen Afirka damar komawa kasuwannin hada-hadar kudi na duniya.

Amma duk da haka, wasu kasashe kamar Jamhuriyar Congo sun tilasta bayar da riba mai tsoka masu tsananin tsada (fiye da kashi 10%), abin da ake ganin bai dace ba ga masu karbar bashi.

Ana hasashen tattalin arziki zai ci gaba da bunkasa a hankali, inda ake sa ran matsakaicin bunkasar GDP zai kai kashi 4.5% a 2026, yayin da gibin kasafin kudi (fiscal deficit) zai ragu kadan zuwa kashi 3.5% na GDP.

Duk da haka, ana sa ran bashin gwamnatoci zai ci gaba da kasancewa a mataki mai tsawo, kusan kashi 61% na GDP a matsakaici.

Karuwar nauyin biyan bashin da ya kai lokacin biya na tilasta wa wasu gwamnatoci neman dabarun sarrafa bashi domin rage hadarin sake aro.

Kasashen da suka fi amfani da wadannan hanyoyi sun hada da Côte d’Ivoire, Benin, Uganda, Jamhuriyar Congo, Mozambique, Kenya da Afirka ta Kudu.