Ziyarar Afirka: Fiye da mutum 500,000 ake sa ran sun halarci taron ibada na Fafaroma Leo a Kamaru

Fafaroma ya saba amfani da irin wannan haɗuwa musamman a ƙasashe masu tasowa, don yi wa matasa wa'azi kan nuna juriya kan matsalolin da suke fauskanta a rayuwa.

By
Páápà Léo yana kira da a samar da ƙarin damammaki ga matasa a Kamaru. / AP

Fafaroma Leo XIV yana dab da cim ma rabin rangadin da yake a ƙasashe huɗu na Afirka a ranar Juma'a, ranar za ta kasance ta ƙarfafa gwiwar matasan Kamaru, da farko a taron ibada sannan da ziyara a jami'ar Katolika ta ƙasar.

A Jumma'ar Leo ya je Douala, gari mai babbar tashar ruwa ta Kamaru, don gudanar da taron ibada da ziyartar asibiti. Fadar Vatican ta yi hasashen mutane kimanin 600,000 za su hallara a wajen ibadar.

Wannan ne taro mafi girma da ake tsammanin Leo zai samu a ziyararsa ta kwanaki 11, wadda ita ce ta farko zuwa Afirka a tarihinsa na kasancewar Fafaroma na farko ɗan asalin Amurka.

A babban birnin Youande, Leo ya gana da ɗalibai, malaman makaranta, da masu gudanarwa a Jami'ar Katolika ta Afirka ta Tsakiya.

Sau da yawa Fafaroma ya saba amfani da irin wannan haɗuwa musamman a ƙasashe masu tasowa, don yi wa matasa wa'azi kan nuna juriya kan matsalolin da suke fauskanta a rayuwa.

Mabiya Katolika suna wakiltar kusan kashi 29% na mutanen Kamaru masu jimillar adadin miliyan 29. Ƙasar tana da matuƙar yawan matasa, inda shekarun tsaka-tsaki na mutane ya tsaya a 18.

Sako ga matasa

Fafaroma Leo ya riga ya yi wa matasan Kamaru kalamai na ƙarfafawa, inda ya yi gargaɗi a jawabin buɗe taron yana cewa, "Tabbas, idan rashin aikin-yi da ƙuncin zamantakewa suka daɗe, fusata na iya kaiwa ga tashin hankali".

Ya ƙara da cewa, "Zuba-jari a ilimi, horo don ƙwarewa, da ƙirƙirar kasuwanci ga matasa, don haka, zaɓi ne na dabaru don zaman lafiya. Shi ne hanya kaɗai don rage kwararar basira zuwa wasu sassan duniya."

Fafaroma Leo ya kuma soki kasashen waje da ke wawashe arziƙin nahiyar Afirka, yana cewa suna taimaka wa wajen yaɗuwar talauci da rashin cigaban ƙasa.

A cewar bayanan Bankin Duniya, adadin marasa aikin-yi a Kamaru ya kai kashi 3.5%, amma kashi 57% na ma’aikata masu shekaru 18 zuwa 35 suna aiki a sashen gamagarin ayyuka.

Matsayin tattalin arziƙi a Kamaru ya haifar da ƙaurar ƙwararru sosai, kuma ya ƙara matsin lamba ga ɓangaren lafiya da ke da ƙarancin ma'aikata, yayin da da yawa daga likitoci da nas ke barin ƙasar don neman ayyuka masu albashi mai tsoka a Turai da Amurka ta Arewa.

A shekarar 2023, kusan kashi ɗaya cikin uku na likitocin da suka kammala karatun likitanci a Kamaru sun bar ƙasar, a cewar Ma'aikatar Ilimi mai Zurfi.