Akalla sojojin Nijar 16 ne suka mutu, yayin da 23 suka jikkata bayan 'yanta'adda sun yi wa tawagar Rundunar Tsaro da Kare Ƙasa (FDS) kwanton-ɓauna a yankin Tillabéri, kamar yadda Ma'aikatar Tsaron Ƙasar ta sanar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen mako, ma'aikatar ta ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Juma'a a kan hanyar Bankilaré-Téra, kusa da ƙauyen Doungouro a yankin Téra, da ke kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso.
A cewar ma'aikatar, sojojin suna kan hanyar zuwa aiki ne a lokacin da suka faɗa cikin abin da ta bayyana a matsayin kwanton-ɓauna mai sarƙaƙiya daga ƙungiyoyin 'yanta'adda masu ɗauke da makamai.
Ta ce an tura da ƙarin sojoji daga Téra tare da taimakon jiragen sama inda suka yi gaggawar kai ɗauki, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.
Ma'aikatar ta ce sojoji 23 sun jikkata a harin, ciki har da tara da suka samu munanan raunuka, waɗanda aka garzaya da su zuwa Asibitin Sojoji da ke Yamai.
Ta ƙara da cewa jami'an tsaron sun kashe 'yanta'adda 15 a yayin artabun.
Haka kuma sun ƙwato babura biyar da maharan ke amfani da su tare da lalata wasu huɗu, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da sintiri domin cafke waɗanda suka tsere.
Wannan sabon harin ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Nijar ke ƙara zafafa hare-harensu a yankin iyakoki uku, inda ƙungiyoyin ‘yanta’adda da ke da alaƙa da EIS da kuma JNIM, mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, suka ƙara yawan hare-haren da suke kaiwa a cikin 'yan shekarun nan.
A sabon rahoton ayyukan soji da Cibiyar Haɗin Gwiwar Ayyukan Soji (CICO) ta fitar a ranar 15 ga Yuli, Rundunar sojin Nijar ta ce ta samu nasarori da dama kan mayaƙan 'yanta'adda da sansanoninsu na ajiye kayayyakin aiki a yankin.
Sojojin sun ce sun kashe 'yanta'adda 19 a wani samame da suka kai a yankin Tinfagatt a ranar 9 ga Yuli. Sun kuma ce sun lalata sansanoni da dama da ake zargin 'yanta'addan ke amfani da su, tare da ƙwato makaman soja, babura, na'urorin hasken rana da sauran kayayyaki.
Makonni kaɗan da suka gabata, jami'an tsaron Nijar sun kuma daƙile wani babban hari da wasu 'yan bindiga masu ɗauke da manyan makamai suka kai a Torodi, kusa da iyakar Burkina Faso. A cewar majiyoyin tsaro da na yankin, an kashe kusan 'yan ta'adda 20, sannan an ƙwato ko lalata kayan sadarwa da kayan aikin soja.

















