| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Ghana ta doke Panama da ci 1-0 a wasansu na farko na Gasar Kofin Duniya
Ƙwallon da Caleb Yirenkyi ya ci ana dab da tashi ya bai wa Ghana nasara da ci 1-0 kan Panama a Rukuni L, a wasan da aka buga a filin wasa na Toronto Stadium da ke Canada a maraicen Laraba.
Ghana ta doke Panama da ci 1-0 a wasansu na farko na Gasar Kofin Duniya
Gana ta doke Panama da ci 1-0 a wasansu na farko na Gasar Cin Kofin Duniya na FIFA na shekarar 2026 a Kanada ranar 17 ga watan Yuni, 2026. / AP

Ghana ta buga wasanta na farko a gasar Kofin Duniya da ke guna a Amurka, Canada, da Mexico, inda wasan na Rukuni L ya gudana a Filin Wasa na Toronto, a Canada a maraicen Laraba.

Kwallo guda da Caleb Yirenkyi ya zura ana dab da tashi ta bai wa Ghana muhimmiyar nasara ta ci 1-0, a kan Panama.

Yirenkyi ya zura ƙwallon a minti na biyar na ƙarin lokaci, wanda ya kawo ƙarshen wata gwagwarmaya mai cike da jan hankali tsakanin tawagogin biyu.

A nan gaba dukkan tawagogin za su fafata da Ingila da kuma Croatia a sauran wasannin rukuni nasu.

A wani wasan da aka buga kafin nan a rukunin, Ingila ta doke Croatia da ci 4-2, inda ɗan wasan gaba na Ingila, Harry Kane, ya zura ƙwallo biyu.

Ghana za ta buga da Ingila wadda a yanzu take kagaba a teburi, ranar 23 Yuni, sannan za ta kammala wasannin matakin rukuni da wasa da Croatia ranar 28 Yuni.

Panama kuma za ta buga da Croatia ranar 24 Yuni, sannan a ƙarshe da Ingila ranar 28 Yuni.