Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce manufofin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa suna ƙara matsi ga Isra’ila da yankin Gabas ta Tsakiya da ma tsaron ƙasashen duniya.
"Manufofin gwamnatin Netanyahu ba su kasance matsala ga mu kaɗai ba," kamar yadda Fidan ya bayyana a wata hira da jaridar The National wadda take a Abu Dhabi ranar Jumma’a. "Manufofinsa da gwamnatinsa sun kasance nauyi ga Isra’ila da yankin da kuma nauyi da barazana ga tsaron duniya."
Fidan ya ce cacar baka tsakanin Ankara da Tel Aviv ba za ta iya rincaɓe zuwa yaƙi ba.
"Babu dalilin yaƙi a bayyane," in ji shi . Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan "shugaba ne na zaman lafiya da hikima" wanda "ba za a iya rinjaya zuwa cikin komai ba," in ji shi .
Shugabannin ƙasashen Turai, yayin da suke fara gane hatsarin Isra’ila, kawo yanzu ba su samu hanyoyin magance matsalar ba, in ji shi, yana mai gargadin cewa ƙoƙarin hamɓarar da ci-gaban da ake samu a Syria zai iya sauya wannan .
Ya ce hankalin ƙasashen duniya ya bar kan Gaza saboda yaƙin yankin Gulf kuma ya ƙara da cewa ana buƙatar ƙarin matsin lamba kan Isra’ila "domin Falasɗinawa su samu ƙarin taimakon jinƙai na ƙasashen duniya."
Fidan ya bayyana matsaya ta musamman ta Turkiyya wajen shiga tsakani a rigingimun yankin.
"Mun san kowa, mun san yadda ko wane rikici yake," in ji shi. "Saboda haka, ina ganin mun fi kasancewa a matsayin iya gane (abubuwan da ke faruwa) da kuma yadda za mu taimaka wajen katse su."
"Ya kamata mu koma wani yanayi na cikakken mutunta ‘yancin kai da kuma martabar ƙasa ta ko wace ƙasa," in ji Fidan. "Iran ta daɗe tana iƙirarin cewa manufar tsaronta ce ta sa take da waɗanda take mara wa baya a cikin waɗannnan ƙasashen, kamar yadda ‘yan Isra’ila suke mamaye sauran wurare a yankin a wani ɓangare na tsaro."
"Idan muka samu wata sabuwar fahimta ta tsaro, wadda za ta tabbatar da aminci da tsaro da kuma ‘yancin kai na siyasa da kuma mutunta ‘yancin iko a kan ƙasa na ko wane ɓangare a yankin, da sabuwar fahimta, ina ganin ya kamata ta shaida wa Iran, duba, za mu iya komawa yankunanmu," in ji shi, yana mai bayyana imaninsa cewa Iran "tana da sanin ya kamatan da ya kai ta gane waɗannan ababen da ke a bayyane."
"Saboda haka cikin fata, idan muka cim ma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, za mu iya fara tattaunawa mai kyau."
Tsagaita wutar Iran da Amurka za ta iya ɗorewa, in ji ministan harkokin wajen Turkiyya
Fidan ya ce shi ya yi imanin cewa tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka za ta iya ɗorewa duk da iƙirarin Shugaban Amurka Donald Trump cewa ta “ƙare."
"Ina ganin an samu rashin tattaunawa da rashin fahimtar juna ne daga ɓangarorin biyu game da yadda ya kamata a aiwatar da wucewa ta mashigar," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa tattaunawa ta waya da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, da yammacin ranar Alhamis ta ba shi "ƙarin fahimta mai zurfi ta tushen matsalar."
Ya ce rage rincaɓerwa lamarin shi ne mafita.
"Ɓangarorin biyu suna son tsagaita wutar kuma suna so su ci gaba da yarjejeniyar zaman lafiya," a cewarsa. "Duk da haka, akwai wani kaso na hatsari da za iya samu, kuma saboda rashin fahimtar juna ko kuma tsokana da ramuwar gayya, dole mu yi mu mayar da hankali sosai."
Da aka tambaye shi game da tattaunawa kan jiragen yaƙi samfurin F35 tsakanin Turkiyya da Amurka, Fidan ya tabbatar da cewa "muradi na siyasar na nan."
Yana mai cewa Trump da Erdogan "sun yanke shawarar cire dukkan cikas da ke toshe hanyar shirin na F-35 " yayin tattaunawarsu a watan Satumba , Fidan ya ce “tun daga wancan lokacin, mun kasance muna aiki a kai."
"Ina ganin za mu cim ma mafita nan ba da jimawa ba," in ji shi.
Ya bayyana cewa Turkiyya ta biya kuɗin jiragen yaƙin "shekaru biyar zuwa shida da suka gabata," kuma suna jira "a cikin wani ginin adana jirage domin” Turkiyya ta ɗauke su.
A shekarar 2019, yayin wa’adin Shugaba Trump na farko, Amurka ta dakatar da Turkiyya daga shirinta na F-35 bayan ta nuna rashin amincewarta ga siyan tsarin tsaron sararin samaniya ta S-400 daga Rasha, tana mai iƙirarin cewa tsaron tsaron sararin samaniyar Rasha zai iya barazana ga jiragen yaƙin.
Turkiyya ta nannata cewa babu wani karo da juna tsakanin tsare-tsaren biyu kuma ta ba da shawarar naɗa kwamitin da zai gudanar da bincike game da lamariun. Ankara ta kuma ce ta sauƙe nauyin da ke a kanta game da jiragen F-35 ɗin kuma dakatar da shirin ya saɓa wa dokoki, tana mai cewa jiragen ba Turkiyya kaɗai za su ƙarfafa ba, har ma da ƙawancen tsaro na NATO.
Da aka tambaye shi game da yiwuwar Turkiyya ta miƙa tsarin tsaron sararrin samaniyar S-400 mga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Fidan ya ce. "Wannan wani yanayi da ake a kai. An yi tattaunawa, tattaunawa a cikin gwamnati."
"Dole a samu tattaunawa mai kyau da ‘yan Rasha," in ji shi, yana mia cewa shi ba zai iya "bayyana sunan ko wace ƙasa ko kuma tsari ko kuma ba wani nau’i na mafita ba a wannan lokaci saboda, kamar yadda na faɗa, akwai mauradi na siyasa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu."
Fidan ya jaddada buƙatar da ke akwia ta haɗa Rasha cikin cikin shirin yiwuwar miƙa S-400 ɗin tun da dai Turkiyya ta saye shi ne daga ƙasar.
















