Masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba biyar sun maƙale a wani ramin haƙar ma’adinai a lardin tsakiyar Zambia bayan ƙasa ta rufta a kansu yayin da suke haƙar ma’adinai, kamar yadda wani baban jami’i ya bayyana ranar Alhamis .
Hukumomi sun bayyana cewa an fara ƙoƙarin kuɓutar da su ranar Laraba, kwana ɗaya bayan aukuwar lamarin, inda aka buɗe rami na farko a wurin haƙar ma’adinan da ke Qon, duk da cewa ba a samu ko mutum ɗaya ba tukunna daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
"Sun buɗe ramin na farko kuma ba su samu ko mutum ɗaya a ciki ba," kamar yadda sakatare na dindindin na lardin tsakiyar ƙasar Milner Mwanakampwe ya shaida wa manema labarai a Kabwe, babban birnin lardin, ranar Alhamis.
Ya ce binciken zai ci gaba kuma gwamnati za ta yi dukkan ƙoƙarinta wajen kuɓutar da masu haƙar ma’adinan da suka maƙale.
Ayyukan ceton da ake yi
"Gwamnatin ta riga kafa kwamiti na sakatarori na dindindin domin nazari game da ayyukan ceton masu haƙar ma’adinan da suka maƙale," in ji shi.
Kwamitin ya haɗa da na ma’aikatar tattalin arziki mai kare muhalli da ta cikin gida da ta kiwon lafiya da kuma ɓangaren ba da agajin gaggawa na ƙasar.
Zambia tana ci gaba da ƙoƙarin daƙile haƙar ma’adinai bai bisa ƙa’ida ba, musamman kan duwatsu masu daraja kamar su zinari, inda aka samu ƙarin wuraren da gwamnati ta ba da lasisin haƙar ma’adinai a ƙasar ta kudancin Afirka da ke da arzikin ma’adinai.
A watan Oktoban shekarar 2025, masu haƙar ma’adinai goma sun mutu, kuma guda biyar sun jikkata bayan wani ramin haƙar madinai ya rufta da su.








