Hukumar CAF ta yi tir da rashin ɗa'a a zagayen kwata-fainal na AFCON 2025
Sakamakon faruwar wasu abubuwa marasa daɗi a wasannin zagayen kwata-fainal, hukumar ƙwallo ta Afirka, CAF ta ce ta fara bincike kan ayyukan rashin ɗa'a da aka gan.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta yi tir da abin da ta bayyana a matsayin halayyar da ba za a amince ba daga 'yan wasa da jami'ai, a yayin wasanni biyu na zagayen kwata-fainal a Gasar Kofin Afirka AFCON 2025 da ke gudana a Maroko.
CAF ta ce tuni ta miƙa lamarin gaban Kwamitin Ladabtarwa na hukumar don gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka faru.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, CAF ta ce ta duba rahotannin wasa da shaidar bidiyo waɗanda suka nuna yiwuwar aikata rashin ɗa'a a lokacin fafatawar zagayen kwata fainal tsakanin Kamaru da Maroko, da kuma Aljeriya da Nijeriya.
Ƙasa mai masaukin baƙi, Maroko ta samu nasarar 3–2 kan Kamaru ranar Juma’a 9 ga Janairu, wasan da aka samu tsananin gogayya, kuma ya ƙare cikin ruɗani yayin da zukata suka harzuƙa bayan tashi daga wasan.
'Yan wasa da dama daga ƙungiyoyin biyu sun yi cacar baki mai zafi a filin wasa, yayin da jami'ai suka shiga tsakaninsu don hana lamarin ƙara ta'azzara, da kuma sanda tawagogin suka nufi hanyar fita.
Zazzafan martani bayan wasa
A ɗayan wasan kwata-fainal ɗin, Nijeriya ta doke Aljeriya da 2–0, wasan da Aljeriya ta soka, inda ta ce sakamakon ya yi muni saboda raunin hukuncin alƙali, ciki har da ƙorafin rashin ba da bugun ɗurme da Aljeriya ta nema.
Fusataccen martani daga 'yan wasa da jami'an Aljeriya ya haifar da rikici kai-tsaye bayan wasan. Ma'aikatan tsaro da jami'an wasa sun shiga tsakani don dawo da doka yayin da aka ga turjiya, da hargitsi kusa da sansanin jami’ai.
Jami’an tsaro sun kewaye alƙalin wasa, Issa Sy da mataimakansa, Djibril Camara da Nouha Bangoura, yayin da suke barin fili. Haka kuma jami'an wasa sun sha wahala wajen riƙe wasu 'yan Aljeriya da suka yi ƙoƙarin kusantar alƙalan.
CAF ta ce an miƙa lamarin da suka faru a duka wasannin zuwa Kwamitin Ladabtarwa, domin gudanar da cikakken bincike, tare da cewa za a ɗauki mataki idan an samu wani da laifi na rashin da'a.
Halayya mara dacewa
Sanarwar ta ce, CAF na yin tir da kowace halayya marar dacewa yayin wasanni, musamman ayyukan da aka nufi jami'an wasa, alƙalai, ko masu shirya gasar. Irin wannan aikin bai dace da tsarin ƙwarewa da aka san gasannin CAF da shi ba.”
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa tana duba hotunan wani lamarin daban da ya shafi wasu 'yan jarida, waɗanda ake zargin sun yi halayya mara dacewa a wajen haɗuwa da 'yan jarida, bayan wani wasan zagayen na kwata-fainal.
CAF ta jadadad aniyarta ta kiyaye ladabi da girmamawa a gasarta, kuma ta ƙarfafa cewa za ta ɗauki mataki mai tsanani don kare gaskiya da mutuncin Gasar Kofin Afirka.