Ronaldo ya dauke jirginsa daga Saudiyya zuwa Madrid bayan harin Iran a Riyadh
Rahotanni sun tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya ɗauke jirginsa na alfarma daga birnin Riyadh na Saudiyya zuwa birnin Madrid na Sifaniya.
Yayin da birnin Riyadh na Saudiyya ke fuskantar hare-hare daga Iran, rahotannin sun tabbatar da gwarzon ɗanwasa Cristiano Ronaldo, ya ɗauke jirginsa daga Riyadh zuwa birnin Madrid na Sifaniya.
Ɗan asalin Portugal, Ronaldo na buga wa ƙungiyar Al Nassr da ke da mazaunin a Riyadh babban birnin Saudiyya, inda ko a ranar Litinin sai da aka kai hari kan pfishin jakadanci na Amurka.
Yayin da aka shiga rana ta huɗu ta Amurka da Isra’ila suka fara kai wa Iran hari, inda Iran ta fara kai harin ramuwa kan sansanonin sojin Amurka a ƙasashen yankin Gulf irin su Saudiyya, da Qatar, Bahrain, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Sakamakon caɓewar lamura a yankin na Gabas ta Tsakiya, al’ummomin ƙasashen waje suna ta tserewa daga yankin don kaucewa rikicin.
Ronaldo da abokiyar zamansa, Georgina Rodriguez da kuma ‘ya’yansu biyar suna zama a Riyadh. Kuma ganin cewa yana da jirginsa na kansa, ana raɗe-raɗin shi ma ya bar Saudiyya ya tafi Turai.
A daren Litinin shafukan masu bibiyar jirage a samaniya sun ambato cewa jirgi samfurin Bombardier Global Express ya kwashe awanni bakwai a sama kafin ya isa Madrid.
Jirgin mai ɗaukar mutum 15 yana da darajar dala miliyan 81, ya bar Riyadh da misalin ƙarfe 8 na dare kuma ya sauka a Madrid da ƙarfe 1 na dare, cewar shafin Flightradar24.
Da ma kuma, Ronaldo yana cikin hutun daga buga ƙwallo saboda ɗage wasannin gasar Zakarun Asiya na zagayen kwata-fainal, sakamakon rikin Gabas ta Tsakiya.