Shugabannin duniya za su dasa itatuwan zaitun a wurin taron sauyin yanayi na COP31 da ake gudanarwa a Turkiyya a ranar 11 ga watan Nuwamba, domin bikin ranar dashen itatuwa ta ƙasa, yayin da za a kafa sabbin dazukan zaman lafiya a dukkan jihohin ƙasar 81.
Daraktan Hukumar Kula da Dazuzzuka ta Turkiyya, Bekir Karacabey, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ranar Litinin cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan ne ya ayyana ranar 11 ga Nuwamba a matsayin ranar dashen itatuwa ta ƙasa a shekarar 2019, inda ya ƙara da cewa an dasa ɗaruruwan miliyoyin itatuwa a faɗin ƙasar tun daga lokacin.
Karacabey ya ce za a gudanar da bukukuwan bana ne ƙarƙashin taken “Numfashi ga Gaba, Zaman Lafiya ga Duniya”, yana mai cewa bikin na bana ya zo da muhimmanci na musamman saboda ya zo daidai da taron ƙasashe na 31 kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (COP31).
“A ranar 11 ga Nuwamba, shugaban ƙasarmu, tare da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya da firaministan Australia, za su dasa itatuwan zaitun a wurin da ake gudanar da taron COP31,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa za a kafa dazukan zaman lafiya a dukkan jihohin ƙasar 81, wanda zai zama mataki na farko na samar da dazukan da ke iya tsotse tare da adana iskar carbon dioxide daga sararin samaniya.
Jama'a za su iya mallakar itatuwan da za a dasa kyauta
Karacabey ya ce 'yan ƙasar za su samu damar shiga ayyukan dashen itatuwa a dukkan jihohin Turkiyya 81, inda za a sanar da wuraren da za a gudanar da aikin ta shafin intanet na Geleceğe Nefes (Numfashi ga Gaba).
Ya jaddada cewa mutanen da ba za su iya zuwa wuraren dashen itatuwan da kansu ba za su iya bayar da gudummawa ga shirin ta hanyar mallakar itacen da za a dasa kyauta a shafin.
“Ina gayyatar dukkan 'yan ƙasarmu da ke jihohi 81 da su halarci wuraren dashen itatuwan da za mu sanar a shafinmu na Geleceğe Nefes. Muna fatan ganin sun zo sun dasa itatuwa,” in ji shi.
“Waɗanda ba za su iya halartar dashen itatuwan da kansu ba za su iya mallakar itacen da za a dasa kyauta ta shafinmu. Ɗaya daga cikin itatuwan da za a dasa zai iya kasancewa nasu, ko kuma su bayar da gudummawar dashen itace.”
‘Komai yana hannunmu’
Karacabey ya jaddada cewa nasarar shirye-shiryen dashen itatuwa ba ta ta'allaka ga yawan itatuwan da aka dasa kawai ba, har ma da yawan waɗanda suka rayu suka girma bayan dasawar.
Ya ce ana sa ido kan ci gaban itatuwan da aka dasa ta hanyar duba su a wuraren da suke, yayin da ake ba su kulawa da kuma sake dasa wasu a wuraren da ya zama dole.
Ya ƙara da cewa ana kuma la'akari da yanayin muhalli da kuma nau'ikan halittu yayin tsara ayyukan dashen itatuwa da zaɓen wuraren da za a dasa su.
Karacabey ya jaddada cewa kare dazuzzuka na buƙatar gudummawar kowa da kowa, inda ya buƙaci 'yan ƙasa su ɗauki matakin hana tashin gobarar daji.
“Mun ce komai yana hannunmu. Za mu iya dasa itace da hannunmu, ko kuma abin takaici mu mayar da itacen da aka dasa toka ta hanyar gobarar da muka kunna,” in ji shi.
“Saboda haka komai yana farawa ne daga gare mu. Muna roƙon 'yan ƙasarmu kada su ce, ‘Me zan iya yi ni kaɗai?’ Eh, za su iya yin abubuwa da yawa. Idan suka kare dazuzzukanmu, dazuzzukanmu ba za su ƙone ba.”
Bisa alkaluman da aka fitar kafin gudanar da bikin, ana sa ran dasa itatuwa guda 1,855,735 a wurare 756 da suka mamaye fili mai girman hekta 2,301 (kadada 5,686) a faɗin ƙasar, yayin da ake sa ran kusan mutum 301,000 za su shiga ayyukan.




















