| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta kama ɗanta'addan FETO da ake nema bisa yunƙurin kashe Shugaba Erdogan a shekarar 2016
Wanda ake zargin, wani kyaftin na soji da aka kora kuma tsohon matuƙin helikwafta, ya kasance ana nemansa ruwa-a-jallo a ƙarƙashin wata Jar Sanarwar ta Hukumar 'Yansandan Duniya.
Turkiyya ta kama ɗanta'addan FETO da ake nema bisa yunƙurin kashe Shugaba Erdogan a shekarar 2016
Wanda ake zargin, wanda aka bayyana da harrufan farkon sunayensa BK, na ɓagaren FETO da ke da hannu a ƙoƙarin kashe Shugaba Tayyip Erdogan. / َAA

Rundunar ‘yansandan Turkiyya ta kama wani mamba na ƙungiyar ‘yanta’adda ta FETO wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa ƙoƙarin kashe shugaban ƙasar a lokacin yunƙurin juyin mulkin da aka ci galaba a kansa a shekarar 2016, in ji ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar.

Wanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da harrufan da ke farkon sunayensa BK, ya kasance cikin ɓangare na ƙungiyar ta’addancin FETO da ke da hannu cikin ƙoƙarin kashe Shugaba Recep Tayyip Erdogan a Marmaris yayin yunƙurin juyin mulkin watan Yulin shekarar 2016, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana ranar Asabar.

Ma’aikatar ta ce wanda ake zargin wani kyaftin na soji ne da aka kora kuma matuƙin helikwafta wanda ake nema ruwa-a-jallo a ƙarƙashin Jar Sanarwar Hukumar ‘Yansandan Duniya.

Ɓangarorin tattara bayanan sirri na ‘yansanda a lardunan Afyonkarahisar da Eskisehir sun ƙaddamar da aiki na haɗin gwiwa da sashen Tattara Bayanan Sirri na Tsaro, in ji ma’aikatar.

Samamen ya gano inda wanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa a matsayin BK, sa’annan ‘yansandan da ke yaƙi da ta’addanci suka kama shi a Afyonkarahisar, a cewar ma’aikatar.

Ma’aikatar ta ce Turkiyya za ta ci gaba da yaƙinta da FETO da muƙarrabanta.

Ƙoƙarin juyin mulkin da aka samu galaba a kansa, inda aka kashe mutum 253 kuma aka raunata 2,734 , FETO ce ta kitsa shi tare da aiwatar da shi a ƙarƙashin shugabanta, Fetullah Gulen.

Rumbun Labarai
Jiragen ruwa biyu na kasuwanci sun yi karo a gabar Tekun Silivri a Istanbul, mutum 10 sun ɓata
30 ga Agusta: Nasarar da ta buɗe hanyar tasowar Turkiyya ta zamani
An haƙo wani sassaƙen ɗan'adam zaune a kan damisa mai shekaru 11,000 a Turkiyya
Turkiyya ta ƙara haɓaka kasuwancin da take yi da ƙasashen Musulmi
Aselsan: Kamfanin tsaro na Turkiyya zai baje-kolin jirgin ƙarƙashin ruwansa a bikin Teknofest
Turkiyya ta ƙaddamar da shirin 2026–2030 na zama cibiyar fasahar AI ta duniya
Trump ya yi 'murna' kan yarjejeniyar tsaro ta Makka da Turkiyya da Pakistan da kuma Saudiyya suka yi
Shugaba Erdogan ya jinjina wa shekara 25 na Jam'iyyar AK kan samar da 'sauyi mai tarihi' a Turkiyya
Shekaru 25 na Jam’iyyar AK da matsayin Turkiyya na mai taka rawa a yanki da ma duniya
Ministan Harkokin Wajen Masar ya gode wa Turkiyya saboda tarban karamci da ta yi wa Mohamed Salah
Turkiyya ta yi kira ga Tunisia da ta saki jagoran Ennahda Ghannouchi da ke tsare a kurkuku
Turkiyya ta kama mutum 30 a wani samame da aka kai kan ƙungiyar masu aikata laifuka ta Alihan
Turkiyya za ta ci gaba da taka rawa da kuma shiga tsakani a Libya, in ji Ministan Harkokin Waje
Cikin hotuna: Turkiyya ta haskaka muhimman wurare don murnar Yajejeniyar Tsaron Hadin Gwiwa ta Makka
An fara gasar baje-kolin jiragen sama marasa matuka ta TEKONOFEST a garin Sirnak na Turkiyya
Erdogan zai kai ziyara Saudiyya don tattaunawa da Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan
Shugaban sadarwa na Turkiyya ya ce Isra'ila na yi wa yunƙurin zaman lafiya na Gaza zagon ƙasa
Turkiyya ta yi fice a Gasar Duniya ta Rubutu a Kwamfuta da kambi 36
Turkiyya da Nijeriya sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa kan ƙera jiragen ruwa
Shugaba Erdogan ya taya tawagar Sultans of Net ta Turkiyya murnar lashe gasar ƙwallon raga ta mata