CAF ta dakatar da kocin Senegal da Achraf Hakimi
CAF ta ci tarar hukumar kwallon kafa ta Senegal dala 615,000 saboda wasu dabi’u da magoya bayan ƙasar suka nuna, yayin da aka dakatar da ’yan wasa kamar Iliman Ndiaye da Ismaila Sarr wasannin CAF biyu saboda wasu dabi’u da suka yi wa alkalin wasa.
Hukumar da ke kula harkokin ƙwallon ƙafa a nahiyar Afirka (CAF) ta dakatar da Kocin Senegal Pape Thiaw wasanni biyar da kuma cinsa tarar dala 100,000 saboda munanan “ɗabi’un da ya nuna” bayan da ya umarci ’yanwasansa da su fice daga filin wasa yayin fafatawar ƙarshe tsakanin Senegal da Maroko a Gasar AFCON.
Sannan CAF ta ci tarar hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal dala 615,000 saboda wasu ɗabi’u marasa kyawu da magoya bayan ƙasar suka nuna yayin da aka dakatar da ’yanwasa — Iliman Ndiaye da Ismaila Sarr — wasannin CAF biyu saboda wasu rashin ɗa’a da suka yi wa alƙalin wasa.
Ko da yake kwamitin ladaftarwa na hukumar CAF ya yi watsi da buƙatar da Maroko ta gabatar kan soke sakamakon wasan bayan ’yanwasan Senegal sun fice daga filin wasa har tsawon mintuna 14.
Kazalika CAF ta ci tarar Maroko dala 315,000 saboda ɗabi’u marasa kyawu da yara masu ɗauko ƙwallo waɗanda aka fi sani da sunan Ball Boys suka nuna yayin wasan, kazalika saboda ɗabi’un wasu ’yanwasa da ma’aikata lokacin da ake kallon bidiyon da yake taimaka wa alƙalin wasa yanke hukunci VAR, da kuma amfani da wata fitila da ke kashe ido da magoya bayan Maroko suka yi.
CAF ta dakatar da kyaftin ɗin Maroko Achraf Hakimi wasanni biyu na CAF, sai ɗanwasa Ismael Saibari da aka dakatar wasanni CAF uku saboda wasu munanan ɗabi’u da suka nuna musamman saboda yadda suka yi yunƙurin cire wani tawul da golan Senegal Edouard Mendy yake amfani da shi.
Kocin Senegal Thiaw ya umarci ’yanwasansa da su fice daga filin wasa bayan da aka soke ƙwallon da suka ci kuma jim kaɗan bayan nan aka bai wa Maroko bugun fenareti ana gab da tashi wasa, ko da yake ɗanwasan Maroko Brahim Diaz ya ɓarar da fenareti.
Sai dai ɗanwasan Senegal Pape Gueye ya yi nasarar jefa ƙwallo a ragar Maroko cikin lokacin da aka ƙara.
CAF ta samu kuɗin shiga masu yawa a gasar kuma an kammala gasar cin nasara ban da hatsaniyar da aka samu a wasan ƙarshen.