Nijar ta ƙaddamar da sabon katin ɗan ƙasa na zamani mai tambarin AES

Manyan jami’an ‘yansandan ƙasar ne suka miƙa masa katin, wanda ake kira CNIB-AES, a gaban ministoci da mambobin majalisar mulki, lamarin da ya nuna fara aikin rajistar jama’a a fadin ƙasar domin maye gurbin tsofaffin katunan takarda.

By
Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya karɓi sabo katinsa na ɗan ƙasa / Nigeria Presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, a ranar Juma’a ya ƙaddamar da sabon tsarin katin shaidar zama ɗan ƙasa na zamani (biometric) bayan karɓar katin farko a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Niamey.

Manyan jami’an ‘yansandan ƙasar ne suka miƙa masa katin, wanda ake kira CNIB-AES, a gaban ministoci da mambobin majalisar mulki, lamarin da ya nuna fara aikin rajistar jama’a a fadin ƙasar domin maye gurbin tsofaffin katunan takarda.

Hukumomi sun ce sabon katin na daga cikin ƙoƙarin Ƙungiyar Ƙasashen Sahel na daidaita takardun shaida da na tafiye-tafiye, inganta tsaro da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashen mambobi.

Jami’ai sun bayyana wannan shiri a matsayin wani babban mataki na zamantar da tsarin katin, inda ake sa ran sabon tsarin zai ƙarfafa tantance mutane da kuma rage yin na bogi.

Ana sa ran fara gwajin samar da katin a watan Afrilun 2026, kafin a fara rabon katunan ga jama’a gaba ɗaya. Katin zai kasance ga ’yan ƙasa masu shekaru 15 zuwa sama, sannan yana da wa’adin shekara biyar zuwa sama, kuma yana ɗauke da matakan tsaro na zamani don kare bayanan mutane.

Gwamnati ta ce wannan shiri ya biyo bayan watanni na shirye-shirye, ciki har da yarjejeniyoyi da kamfanonin fasaha domin samar da kayayyakin aiki na rajistar katin na zamani da kuma kula da bayanai cikin tsaro. Ana kuma sa ran gina cibiyar bayanai ta zamani da tsarin tabbatar da sahihanci mai ƙarfi.

Hukumomi sun ƙara da cewa sabon katin zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro a ƙasa da ma yankin gaba ɗaya, ta hanyar samar da ingantacciyar hanyar tantance ’yan ƙasa, musamman a yankin da ke fuskantar matsalolin tsaro da barazanar ƙetare iyakoki.

An ƙera katin CNIB-AES da robar polycarbonate mai inganci, wanda ya dace da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, inda jami’ai suka ce wannan mataki na nuna gagarumin ci gaba na zamani da inganta tsarin rajistar jama’a a Nijar.