NACA ta yi gargadi game da yaɗa bayanan HIV ba bisa ƙa'ida ba a shafukan sada zumunta a Nijeriya
A wata sanarwa da Darakta Janar na NACA, Dr. Temitope Ilori ya sanya wa hannu, hukumar ta ce ba ta a amince da rahoton ba kuma bai bi tsarin da ake bukata ba don neman izini da kuma wallafa bayanan da suka shafi cutar HIV.
Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki a Nijeriya wato NACA ta ce ita kaɗai ce hukumar gwamnati da aka ba izini a hukumance kuma wadda ta cancanci samar da bayanai da kimanta alkaluman cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV a Nijeriya.
Hukumar ta bayyana da hakan ne biyo bayan wani rahoto wanda ba a ba da izini a kansa ba ya yadu a shafukan sada zumunta kana yana dauke da alkalumar cutar ta HIV daga jiha zuwa jiha na watan Janairu zuwa Maris na 2026.
A wata sanarwa da Darakta Janar na NACA, Dr. Temitope Ilori ya sanya wa hannu, hukumar ta ce ba ta a amince da rahoton ba kuma bai bi tsarin da ake bukata ba don neman izini da kuma wallafa bayanan da suka shafi cutar HIV.
NACA ta bayyana cewa bai kamata ana daukar bayanai kan HIV da kuma yada shi ba tare da an tantance shi sosai ba, tana mai kari da cewa akwai tsauraran ka'idoji da ya kamata a bi don tabbatar da cewa an fassara irin wadannan bayanai sosai da kuma isar da su ga al’umma.
Hukumar ta kuma kara da cewa, duk da cewa bayanan alkaluman da ke cikin rahoton sun nuna cewa an dauke su ne daga Ma'ajiyar Bayanai na Kasa na hukumar, sun yi nuni kan sakamakon cutar ne kawai daga gwajin da ake yi akai-akai a cibiyoyin lafiya kana ba sa wakiltar ainihin alkaluman yawan wadandan suke dauke da cutar HIV daga kowace jiha.
A cewar NACA, bai kamata a rikita bayanan yawan masu dauke da cutar HIV ko kuma wadanda suka kamu da ita ba wajen tantance yawan masu cutar a matakin jihohi ba.
Sanarwar ta kara cewa bambance-bambancen da ke cikin alkaluman na iya hada wa yawan jama'a, da matakin gwajin da aka gudanar, da kuma gibin da ke tsakanin rahotanni da ake samu.
Saboda haka, hukumar NACA ta ƙaryata duk wasu bayanai da aka yada a matsayin alkalumar cutar, kuma ta shawarci mutane da kungiyoyi da ke neman bayanai masu alaka da HIV da su gabatar da bukatunsu a hukumance ta hanyoyin da suka dace.
Ta kuma yi kira ga jama'a da su yi watsi da labaran da ke yawo wadanda ba su da sahihanci, tana mai gargadin cewa amfani da bayanan lafiyar jama'a ba bisa ka'ida ba na iya haifar da rudani da kuma kawo cikas ga kokarin da ake yi na shawo kan cutar HIV/AIDS a Nijeriya.