‘Yansanda a Nijeriya sun musanta an yi garkuwa da masu Ibada fiye da 100 a Kaduna
Kwamishinan ‘yansandan jihar Kaduna da ke Nijeriya, Muhammad Rabiu, ya bayyana cewa jita-jita ce da masu tayar da rikici ke yaɗawa cewar wai an yi garkuwa da masu Ibada fiye da 100 a ƙaramar hukumar Kajuru.
Rahotanni masu cin karo da juna a ranar Litinin sun bayyana cewa a ‘yanbindiga sun yi garkuwa da masu ibada fiye da 100 a wani coci na ranar Lahadi a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru.
Sai dai kuma, da yake zanta wa da manema labarai a ranar Litinin bayan Zaman Majalisar Tsaro ta Jiha a Gidan Sir Kashim Ibrahim, Kwamishinan ‘yansandan jihar Kaduna ya ƙalubalanci masu yaɗa wannan labari da su kawo sunayen waɗanda aka yi garkuwar da su.
Ya gargaɗi waɗanda ya kira da masu yaɗa labaran ƙanzon kurege da su daina ƙoƙarin kawar da zaman lafiyar da aka samu a jihar Kaduna, yana mai cewa za a binciko da kama masu yaɗa waɗannan ƙarerayi.
Shi ma da yake jawabi, shugaban ƙaramar hukuma Kajuru, Dauda Madaki, ya bayyana cewa bayan jin jita-jitar kai harin, ya tura ‘yansanda da sauran jami’an tsaro zuwa Kurmin Wali inda ba su ga alamun wani kai hari ba.
“Mun ziyarci cocin da aka ce an yi garkuwa da mutanen. Babu wata alama ta aukuwar hakan. Na tambayi Dagacin ƙauyen, Mai Dan Zaria, ya kuma tabbatar da cewa babu wani hari da aka kai,” in ji Madaki.
Ya ci gaba da cewa “Na kuma kira shugaban matasan yankin, Bernard Bona, wanda ‘yanjarida suka yi hira da shi, ya kuma ce babu wani abu makamancin haka da ya auku. A saboda haka ina ƙalubalantar duk wani da yake da sunayen waɗanda aka yi garkuwa da su ya kawo su. Tuntuni nake jiran sunayen amma babu wanda ya kawo su.”
Ya ce yana zargin wasu da ba sa jin daɗin zaman lafiyar da aka samu a Kajuru tun bayan zuwan wannan gwamnatin ne ke yaɗa labarin na ƙanzon kurege.
Shugaban ya shawarci jama’a da su nutsu su ci gaba da ayyukansu na yau da kullum, yana mai kira a gare su da su sanar da jami’an tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ko kuma masu yaɗa jita-jita.
Shi ma da yake cewa wani abu, Kwamishinan tsaron Cikin Gida Suke Suaibu (SAN), ya ce shugabannin CAN da sauran jagororin addini sun gana da jama’ar yankin da ake cewa an kai harin, sun kuma bayyana cewa duk abin da ake bayyanawa ƙarya ce tsagwaronta.