Trump ya hana Afirka ta Kudu zuwa taron 2026 a Miami
Trump ya yi ishara ga iƙirarinsa na "kisah kiyashi" kan fararen fata a Afirka ta Kudu da kuma yadda ta ƙi miƙa shugabancin G20 ga Amurka a matsayin dalilan da suka sa ya hana ƙasar zuwa taron na bara.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi shelar cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na bana a Miami ba, inda ya ɗaga rikicin diflomasiyya kan ƙasar zuwa wani sabon mataki.
Trump ya yi ishara ranar Laraba ga abin da ya kira "keta haƙƙin bil’adama mai muni" da manoma fararen fata suka fuskanta, da kuma yadda Afirka ta Kudu ta ƙi miƙa shugabancin G20 a ƙarshen taron ga Amurka.
"Afirka Ta Kudu ta nuna wa duniya cewa ba ƙasa ce wadda ta cancanci kasancewa mamba a ko ina ba," kamar yadda Trump rubuta a shafinsa na Truth Social.
Gwamnatin Trump ta ƙi halartar taron G20 na wannan shekarar, wanda aka ƙarƙare kwanan nan a Johannesburg, tana mai cewa ababuwan da Afirka ta Kudu ta mayar da hankali kansu ciki har da haɗin kai kan kasuwanci da yanayi, sun ci karo da manufofinta.
Shi kuwa Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ƙi miƙa shugabancin G20 a hukumance ga ƙasar da za ta karɓi baƙuncin taron a gaba, wato Amurka, kamar yadda aka saba.
Jami’an Trump sun kuma yi zargi mara tushe na “kisan ƙare dangi kan fararen fata” da ya mayar da hankali kan ‘yan ƙabilar Afrikaners, zuri’ar Turawan da suka fara kama wuri suka zauna, a Afirka ta Kudu.
"Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ƙi amincewa da ko kuma magance keta hakkin ɗan’adam mai muni ga ‘yan ƙabilarnAfrikaner da sauran zuri’ar ‘yan Dutch da Faransa da Jamus da suka zauna [a wurin]," kamar yadda Trump ya rubuta a saƙon da ya wallafa ranar Laraba. "[Bari na] bayyana ƙarara, suna kashe fararen fata, kuma suna bari ana ƙwace gonakinsu."
Daga baya, Ramaphosa ya bayyana rashin jin daɗinsa game da kalaman Trump, in ji ofishinsa.
A watan Mayu, a cikin Fadar White House, Shugaba Trump ya shammaci Ramaphosa ta hanyar nuna masa wani bidiyo mai cike da kurakurai, wanda yake tunanin yana tabbatar da zarge-zargensa, lamarin da Afirka Ta Kudu ta musanta.
Taron G20, wani taro mai tara ƙasashe 20 da suka fi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya, za a yi shi ne a watan Disamban shekarar 2026, a wajen shaƙatawa na wasan Golf na Miami a Florida, wanda mallakin iyalan Trump ne.