Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana muhimmiyar rawar da Turkiyya ke takawa a yayin da ake tsaka da fama da rikicin tattalin arziki a faɗin duniya.
"Manyan masu ruwa da tsaki a al’amuran duniya sun karɓi hakan - wani lokaci cikin sakewar rai amma mafi yawan lokuta saboda ba yadda suka iya - ba za a iya kafa wani yanayi da bai haɗa da Turkiyya ba, kuma ko da haka ne, ba ta da damar wanzuwa," in ji Erdogan a ranar Laraba yayin taron ƙungiyar AK Party a Ankara.
Erdogan ya kuma yi gargadi game da yadda rikicin kasuwanci ke ci gaba da ruruwa, wanda ake sa ran zai sake ɓarkewa a duniya.
"An fahimci cewa yaƙin kasuwanci da haraje-harajen kwastam suka jawo zai yi mummunan tasiri a duniya. Guguwar wannan lamari sai ta shafi kowa da kowa," in ji shi.
Rashin tabbas a duniya
Yayin da yake tabbatar da ɗaukakar da Ankara ke samu, Erdogan ya ce: "Ba a al’amuran manyan ƙasashe kawai Turkiyya ke taka rawa ba, ta zama wata muhimmiyar ƙasa wajen kawo sauye-sauye.”
Ta fuskar tattalin arziki, Erdogan ya bayyana kwarin gwiwar cewa matsayin Turkiyya zai taimaka mata wajen tunkarar kalubalen da ke gabanta.
"Yayin da muke cikin kasashen da aƙa ƙara musu haraji amma ƙadan, mun yi imanin za mu shawo kan wannan ƙalubalen cikin sauki idan aka kwatanta da sauran kasashe."
Ya kuma ba da tabbaci ga 'yan kasuwar Turkiyya a halin da ake ciki na rashin tabbas a duniya.
A ranar 10 ga Fabrairu, Trump ya ba da sanarwar kakaba harajin kashi 25 cikin 100 kan ƙarafa da alminiyom, matakin da ya sha alwashin inganta masana'antu na kasa da masu ƙere-ƙere a Amurka.












