Me ya sa Trump yake ganawa da shugabannin Afrika biyar a Fadar White House?
Wannan ganawar na zuwa ne a lokacin da Amurka ke sauyawa daga mu'amalar ba da talllafi zuwa kasuwanci, tana mai kallon damarmakin zuba jari da alaƙar tsaro a yankin, inda China da Rasha ma ke faɗaɗa ƙarfin faɗa a jinsu a can.
Shugaban Amurka Donald Trump zai tarbi shugabannin kasashe biyar na Afirka a wata liyafar abincin rana a Fadar White House ranar 9 ga watan Yuli, inda ake sa ran batutuwan kasuwanci da cinikayya za su kasance a gaba-gaba cikin abubuwan da za a tattauna.
Shugabannin ƙasashen Senegal, Liberia, Guinea-Bissau, Mauritania, da Gabon za su gana a ɗakin cin abincin gwamnati na Fadar White House domin tattauna batutuwan cinikayya, zuba jari, da tsaro, da sauran al’amura, kamar yadda jami’ai suka shaida wa AFP.
Sai dai, ba a bayyana cikakkun bayanai game da manufar Fadar White House ba.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke mayar da hankali kan haraji da yarjejeniyoyin cinikayya, tare da neman tabbatar da samun isassu ma’adanai masu muhimmanci.
Amma kasashen biyar ba su da arzikin ma’adanai mai yawa kamar wasu kasashen Afirka, irin su Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
Taron ya zo ne kwanaki kadan bayan gwamnatin Trump ta yi murnar rufe hukumar bayar da tallafin ƙasashen waje ta Amurka, USAID, tana mai bayyana hakan a matsayin kawo karshen tsarin “dogaro da tallafi.”
Jami’an kasashen biyar da suka yi magana da AFP sun bayyana fahimtarsu game da manufofin Fadar White House.
Shugaban Liberia Joseph Boakai ya karbi gayyatar da nufin ganin kasarsa ba za ta kasance mai dogaro da tallafi kawai ba, kamar yadda sakatariyar yada labaransa, Kula Fofana ta shaida wa AFP ranar Talata.
“Manufarmu ita ce mu mayar da hankali kan cinikayya da abokan huldar da za su zuba jari,” in ji ta.
Kakakin Shugaban Ƙasar Gabon, Theophane Biyoghe ya ce ganawar wata dama ce don samar da hadin kai “wanda ya mayar da hankali kan masana’antar tattalin arzikinmu.”
Gasa da tsaro
Abokan hamayyar Amurka, wato China da Rasha, sun samu gagarumin tasiri a yankin a baya bayan nan, ciki har da gagarumin zuba jari da Beijing ta yi a wasu kasashe.
A daya bangaren kuma, Moscow ta bayar da goyon baya ga sabuwar Kungiyar Kasashen Sahel (AES) da aka kafa, wadda ta ƙunshi Mali, Burkina Faso, da Nijar.
Kasashen kungiyar suna maƙwabtaka da wasu daga cikin kasashen da za su halarci liyafar ta ranar Laraba.
Kafin ya tafi Washington, Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya bayyana ziyarar ga manema labarai a matsayin “mai matuƙar muhimmanci” ga ƙasarsa.
“A bangaren tattalin arziki, wannan wata babbar dama ce da ke buɗe mana kofa,” in ji shi, yana mai fatan kasarsa za ta amfana daga “goyon bayan” da Amurka ke bayarwa ga sauran kasashe.
‘Ziyarce-ziyarcen da ba su da tabbas’
Wasu shugabannin duniya sun fuskanci matsaloli masu tsanani yayin ziyararsu a Fadar White House.
Daga cikinsu akwai Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.
A lokacin wata ziyara, Trump ya nuna wa shugaban Afirka ta Kudu wani bidiyo da ke dauke da ikirarin karya na “kisan kare dangi na fararen fata” da ake zargin ana yi a ƙasarsa.
Duk da cewa wadannan abubuwan sun faru ne a gaban kyamarori a Ofishin Oval, har yanzu ba a tsara ko shugabannin kasashen Afirka biyar da za su gana da Trump ranar Laraba za su bayyana a gaban manema labarai ba.