| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Sarkin Katsinan Gusau, Dakta Ibrahim Bello ya rasu
Sarkin ya rasu yana da shekara 71 a wani asibiti da ke Abuja babban birnin Nijeriya kamar yadda Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya ya tabbatar.
Sarkin Katsinan Gusau, Dakta Ibrahim Bello ya rasu
An naɗa Dakta Ibrahim Bello Sarkin Gusau na 15 a ranar 16 ga watan Maris ɗin 2015, a zamanin gwamnan Abdulaziz Yari. / TRT Afrika Hausa

Sarkin Gusau Alhaji Dakta Ibrahim Bello wanda aka fi sani da Sarkin Katsinan Gusau ya rasu.

Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya FRCN ne ya tabbatar da rasuwar a safiyar Juma’a.

Ya rasu yana da shekara 71 a wani asibiti da ke Abuja babban birnin Nijeriya.

An naɗa Dakta Ibrahim Bello Sarkin Gusau na 15 a ranar 16 ga watan Maris ɗin 2015, a zamanin gwamnan Abdulaziz Yari.

Ya gaji ɗan uwansa Alhaji Muhammad Kabiru Danbaba wanda ya rasu a wani asibiti a Abuja a ranar 5 ga Maris ɗin 2015, kamar yadda gidan rediyon FRCN ya tabbatar.