Ƙaruwar farashin mai saboda yaƙin Iran zai shafi muhimman sassa na Afirka, in ji jami'a a nahiyar
Masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziƙi a ƙasashen Afirka daban-daban sun yi gargaɗin cewa yaƙin da ake yi a Iran zai jawo ƙalubale ga tsarin hada-hadar kuɗi da kuma shafar manyan sassa kamar hakar ma'adanai
Hukumomi a ƙasashen Afirka daban-daban sun yi gargaɗin cewa tashin gwauron zabi na farashin mai sakamakon rikici a Iran zai jawo ƙalubale ga tsarin hada-hadar kuɗi da kuma shafar manyan sassa kamar hakar ma'adanai, wanda zai sa farfaɗowar tattalin arziƙin yankin ya zama cikin hatsari.
Manyan bankunan ƙasashe daga Accra har zuwa Luanda sun rinƙa rage kuɗin ruwa na bashi a 'yan watannin baya saboda raguwar hauhawar farashi da kuma samun daidaito a musayar kuɗin waje, da kuma don ƙarfafa tattalin arzikinsu.
Wataƙila wannan ya tsaya, aƙalla a yanzu.
“Lokutan rashin tabbas da suka ƙaru sun zama siffa ta yanayin tattalin arzikin duniya, inda suke ƙalubalantar manyan bankuna na ƙasashen duniya a hanyoyi daban-daban,” kamar yadda Babban Bankin Uganda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Karin haɗari
Bankin, wanda shi ne bankin kaɗai da ya ɗauki matakai na taka-tsantsan tun kafin yaƙin ya ɓarke, ya ce zai sake duba tsare-tsarensa don tabbatar da ingancinsu a irin wannan mawuyacin yanayi.
Babban Bankin Angola ya dakatar da rage kuɗin ruwa a ranar Alhamis bayan an yi irin wannan ragi sau uku a jere, inda Gwamna Manuel Tiago Dias ya ambaci ƙarin haɗari.
“Waɗannan haɗarurruka sun fi tasowa ne daga yiwuwar tsawaita yaƙin da ake yaki a Gabas Ta Tsakiya, wanda zai iya shafar hanyoyin jigilar kayayyaki, musamman kayan aikin gona da takin zamani,' in ji shi.
Masana sun ce sauran manyan bankunan duniya za su buƙaci sake duba matakai, inda ake sa ran Ghana, Nijeriya, Zambia da Kenya za su sake duba tsarinsu na rage kuɗin ruwa.
An rage hasashen
JPMorgan ya rage hasashen rage hasashensa a kan Nijeriya, Kenya, Ghana da Zambia, yana danganta hakan ga rikicin.
“Sai dai Angola, mun rage yawan ragin da aka tsara a baya,” kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa ta bincike.
Farashin danyen mai na Brent ya kasance ƙasa kaɗan da dala 100 a kowace ganga a ranar Juma'a, bayan ya kai kusan dala 120 a farkon makon.
“Idan matsakaicin farashin mai ya kasance a kan dala 100 a shekara, za mu ga raguwar kuɗaɗen ƙasashe na nahiyar da ke waje kuma kuɗaɗen ƙasashe da dama za su rage daraja da kashi 5 cikin 100,” in ji Charlie Robertson, wanda shugaban manyan dabaru ne a FIM Partners.
Manyan Bankuna na Kenya, Nijeriya, Ghana da Zambia ba su mayar da martani ga buƙatun sharhi ba.
Kenya, mai shigo da mai fiye da fitarwa, ta ga ga raguwa a takardun lamuninta tun bayan barkewar rikicin. Amma hukumomi sun ce a yanzu man fetur ya wadata.