Isra'ila na dab da halasta hukuncin kisa kan fursunoni Falasɗinawa
Ƙudirin dokar Isra'ilar zai ba da damar aiwatar da hukuncin kisa a kan Falasɗinawa da aka kama, inda zai buƙaci a aiwatar da hukuncin cikin kwanaki 90.
Kwamitin tsaron ƙasa na Majalisar Dokokin Isra’ila ya amince da wani daftarin doka da yammacin Talata a wani mataki na halasta aiwatar da hukuncin kisa kan fursunoni Falasɗinawa.
Ana sa ran za a gabatar da ƙudirin a zauren Majalisar Dokokin ƙasar a mako mai zuwa domin ƙada ƙuri’a a karatu na biyu da na uku, matakai na ƙarshe kafin daftarin ya zama doka.
Kwamitin ya yi gyararraki ga ƙudirin wanda ya tsallake ƙuri’arsa ta farko, kamar yadda kafar watsa labaran gwamnatin Isra’ila KAN ta ruwaito, tana mai ƙarawa da cewa za a iya aiwatar da hukunce-hukuncen kisa ta hanyar rataya.
Za a saka waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa a wata cibiyar ajiye fursunoni ta daban ne inda ba za a ba su damar kai musu ziyara ba tare da neman yardar jami’an da aka bai wa damar yin hakan ba, kuma za su iya tuntuɓar lauya ba sai dai ta bidiyo.
Dole a aiwatar da hukuncin kisa cikin kwanaki 90 da yanke hukuncin.
Ƙudirin ya bayyana cewa za a iya ƙaƙaba hukuncin kisan ba tare da masu gabatar da ƙara sun nemi a yi hakan ba, kuma ba dole sai alƙalai sun haɗa baki ba kafin a yanke hukuncin kisan, kuma alƙalai masu rinjaye za su iya yanke hukuncin kisa.
Babu ɗaukaka ƙara
Ga Falasɗinawan da ke ƙarƙashin mamayar Isra’ila da ake yanke wa hukuncin kisa, ƙudirin ya ce za a rufe damar afuwa ko ɗaukaka ƙara .
Ga fursunoni da aka yi wa shari’a a cikin Isra’ila za a iya rage hukuncin kisan zuwa ɗaurin rai da rai.
Ministan tsaron ƙasar Isra’ila mai ra’ayin riƙau Itamar Ben-Gvir ya yi maraba da ƙudirin, wanda ya bayyana shi "a matsayin wata rana mai cike da tarihi."
Tun lokacin da ta fara yaƙin ƙare-dangi kan Gaza a watan Oktoban shekarar 2023, Isra’ila ta zafafa cin zarafin fursunoni Falasɗinawa, musamman waɗanda suke daga zirin Gaza.
Ƙungiyoyin kare hakkin biladama sun ba da rahoton azbtarwa da yunwatarwa da cin zarafi da kuma hana su samun kulawar ma’aikatan jinya.