| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Danwasan Chelsea, Mudryk, ya dawo kwallo bayan dakatarwar kwana 600 bisa laifin shan kwayoyin kuzari
A Nuwamban 2024 ne aka gano haramtaccen sinadarin meldonium a jikinsa, wanda a ƙa’ida ana amfani da shi don maganin cutukan zuciya amma yana iya inganta kuzari da farfaɗowa ga ‘yanwasan motsa-jiki.
Danwasan Chelsea, Mudryk, ya dawo kwallo bayan dakatarwar kwana 600 bisa laifin shan kwayoyin kuzari
Mykhailo Mudryk ɗan asalin Ukraine ne mai shekaru 25.

Ɗanwasan Chelsea, Mykhailo Mudryk ya dawo buga ƙwallo bayan ya kammala dakatarwar da aka hukunta masa sakamakon samun sa da laifin ta’ammuli da ƙwayoyin ƙara kuzari.

Mudryk ya dawo tawagar Chelsea ƙarƙashin sabon koci, Xabi Alonso, inda ya halarci tafiye-tafiyen ƙungiyar gabanin fara sabuwar kaka, inda suka je Australia da kudu masu gabashin Asiya.

Wa’adin dakatarwa ya ƙare ne a ƙarshen makon da ya wuce, kuma hakan na zuwa ne kimanin shekara ɗaya da watannin takwas, wato kwanaki 614 bayan buga wasansa na ƙarshe a Chelsea.

Ɗan asalin Ukraine, Mudryk ɗan wasan gaba ne ta gefe mai shekaru 25 a duniya. A yanzu ya samu ‘yancinsa kuma ya cancanci shiga filin wasa ya buga ƙwallo.

Sai dai duk da dawowarsa filin ƙwallo akwai babbar alamar tambaya kan makomarsa a Chelsea da ma a fagen ƙwallon bagadaya.

Chelsea da kocinta Alonso sun ambata cewa za su taimaka masa wajen sake sabawa da ‘yan ƙungiyarsa, da kuma farfaɗo da kuzari da tagomashinsa a filin wasa.

Tun da fari Hukumar ƙwallo ta Ingila, FA ta dakatar da Mudryk na wucin-gadi kafin ta ba shi dakatarwar shekaru huɗu, bayan ta gano wani sinadari a jikinsa wanda aka haramta amfani da shi.

Sansantawa da hukumomi

A Nuwamban 2024 ne aka gano haramtaccen sinadarin meldonium a jikinsa, wanda a ƙa’ida ana amfani da shi don maganin cutukan zuciya amma yana iya inganta kuzari da farfaɗowa ga ‘yanwasan motsa-jiki.

A farkon shekarar nan ne Mudryk ya ɗaukaka ƙara a kotun warware jayayya kan wasanni (CAS), amma sai a yanzu aka warware batun dakatarwar tsakaninsa da FA da kuma Hukumar hana amfani da ƙwayoyin kuzari (WADA).

Hakan ya faru ne bayan Mudryk ya amsa cewa ya karya dokar ƙwayoyin kuzari sannan ya amince da dakatarwa daidai da lokacin da ya riga ya kwashe a zaune, wanda ya ba shi damar dawowa buga ƙwallo nan-take.

Haka nan an ƙaddamar da sabbin sauye-sauye a dokar ƙwayoyin kuzari, wadda ke nufin idan aka samu ƙanƙanin sinadarin meldonium a gwajin fitsarin ɗanwasa a yanzu ba zai janyo masa dakatarwa ba.

Tuni Mykhailo Mudryk ya wallafa saƙon murnar dawawarsa fili inda ya bayyana godiyarsa yana cewa a shafinsa, "yaƙi mai tsawo" ya kawo ƙarshe. Wannan ya kasance mafi tsananin yanayi a rayuwata ta wasa".

Sai dai ya kuma jaddada cewa, "kamar yadda na sha nanatawa tun daga farkon wannan batu, ni ban sha wani abu da gangan da na san haramtacce ne ba ne."